Darika da Izala: Sheikh Mansur Isa Yelwa Ya 'Ajiye' Limanci a Jami'ar ATBU
- Sabani ya bayyana tsakanin al'ummar Musulmi a jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi kan mallakar masallaci
- Farfesa Mansur Isa Yelwa da ya shafe shekaru yana limanci a masallacin jami'ar ya sanar da ajiye jagorantar masallacin makarantar
- Malamin ya bayyana cewa ya dauki matakin ne domin kare makarantar da fadawa wani rikici da zai iya kawo rabuwar kan Musulmi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Babban limamin masallacin jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi, Farfesa Mansur Isa Yelwa ya ce ya ajiye limanci.
Duk da shafe shekaru yana limamci a masallacin jami'ar, malamin ya ce ya fahimci ajiye limancin ne ya fi dacewa idan har makarantar bata sauya matsaya ba.

Source: Facebook
A wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Mansur Isah Yelwa ya ce ajiye aikin da ya yi nada alaka da shirin kafa sabon masallaci a jami'ar.
Mansur Isa Yelwa ya ajiye limanci
Bayan shafe sama da shekara 17 yana limanci a jami'ar ATBU, Farfesa Mansur Isa Yelwa ya ajiye mukamin da aka ba shi matukar ba a dauki matakin gyara ba.
Hakan ya biyo bayan matakin samar da fili domin gina masallaci da jami'ar ta yi ga 'yan Darikar Tijjaniyya ba tare da tuntuba ko sanar da shi ba.
Malamin ya bayyana cewa hakan bude kofa ce ga raba kan al'ummar Musulmi da suke cikin jami'ar kasancewar babu wani masallaci da ke da alaka da wata kungiyar addini.
Farfesa Yelwa ya bayyana cewa babbar manufar limancinsa a masallacin shi ne samar da hadin kai tsakanin al'ummar Musulmi.
Yayin da ya ke nuna cewa bai taba samun sabani da 'yan darika ba, malamin ya ce:
"Ina godiya ga Allah da ya sa tunda na fara limanci ban samu sabani da kowa ba,"
Ya kara da cewa bai ga dalilin da zai sanya a dauku irin matakin ba tare da an sanar da shi ba ko kuma a nemi shawarin shi, wanda ya ce hakan ya nuna shi fanko ne ba liman ba.

Source: Facebook
Barazanar yawaitar masallatai
Malamin ya bayyana cewa ba shi da matsala da 'yan darikar Tijjaniyya a kan ibada da za su yi, sai dai ya ce hakkin shi ne a matsayin shi na liman ya lura da harkokin masallatai a makarantar.
A kan haka ya ce bai yarda da cewa a ba wata kungiya masallaci ba saboda bayan Tijjaniyya akwai darikar Qadiriyya, Izala da 'yan shi'a.
Ya bayyana cewa hakan zai bude kofa ga sauran kungiyoyi su rika bukatar a ba su fili su gina masallaci a cikin jami'ar, wanda zai kara raba kan jama'a.
Malamin ya ce da kan shi ya dakatar da 'yan agajin Izala daga zuwa masallacin saboda kar a ce ya Izalantar da shi, inda ya ce ba a barin kowane dan kungiya ya yi abin da ya kebanta da shi a wajen ibadar jami'ar.
An tallafi malamar Islamiyya
A wani labarin, mun kawo muku cewa ustazai da malaman Islamiyya a Najeriya sun hada kudi domin tallafawa iyalan malamar da aka kashe a Kaduna.
Shugaban tafiyar, Abdulkarim Hamisu Assuyudi ya bayyana cewa sun hada kudi sama da N250,000 domin tallafawa 'ya'yan marigayiyar.
Wasu mutane ne suka kashe malama Ummulkhairi yayin da ta ke kan hanyar zuwa wajen karatu a jihar Kaduna bisa zargin tana satar yara a Maraban Jos.
Asali: Legit.ng


