Manyan Abubuwa 4 da Ka Iya Ruguza Yarjejeniyar Kasar Musulunci Ta Iran da Amurka
A makonnin da suka gabata ne Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran suka kulla yarjajeniyar farko kan yadda za a kawo karshen yakin da ya barke tsakaninsu a Gabas ta Tsakiya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Idan ba ku manta ba Amurka tare da hadin gwiwar Isra'ila sun yi yaki mai tsanani na tsawon fiye da kwanaki 40 da Iran, lamarin da ya jawo asarar dubban rayuka da dukiyoyi masu tarin yawa.

Source: Getty Images
Tashar CNN ta ruwaito cewa bayan shafe makwanni ana tattaunawa, Amurka da Iran sun cimma matsaya ta farko kan hanyar kawo ƙarshen rikicin da ya jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin tashin hankali.
Kasashen Iran da Amurka sun cimma matsaya
An ruwaito cewa Shugaba Donald Trump na Amaurka da takwaransa na Iran, Masoud Pezeshkian, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna mai ɗauke da sharuɗɗa 14.
Wannan yarjejeniya ita ake fatan za ta zama wani tsani da zai share fagen cimma yarjejeniya ta ƙarshe cikin kwanaki 60.
Yarjejeniyar ta ƙunshi matakan sassauta takunkumai kan Iran, sake buɗe hanyoyin kasuwanci da jigilar mai ta mashigar Hormuz, da kuma kafa wata gidauniya ta dala biliyan 300 domin taimaka wa tattalin arzikin Iran ya farfaɗo.
Abubuwan da za su iya ruguza yarjejeniyar
Sai dai duk da wannan ci gaba, masana sun yi gargadin cewa akwai manyan matsaloli da za su iya hana yarjejeniyar da aka cimma kai wa ga nasara.
Legit Hausa ta tattaro muku muhimman abubuwa hudu da ka iya dawo da hannun agogo baya a yunkurin kasashen na kawo karshen wannan yaki gaba daya, ga su kamar haka:
1. Kai hare-hare Lebanon
Ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke gaban yarjejeniyar shi ne rikicin da ke ci gaba da gudana tsakanin Isra'ila da ƙungiyar Hezbollah a Lebanon, cewar rahoton BBC.
Ƙungiyar Hezbollah tana da kyakkyawar alaƙa da Iran, kuma ta shiga yakin ne bayan hare-hren farko da Amurka da Isra'ila suka kaddamar a karshen watan Fabrairun 2026.
To sai dai duk da yarjejeniyar ta tanadi dakatar da ayyukan soji a yankin, Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare a wasu sassan Lebanon.

Source: Getty Images
Iran ta dage cewa kawo ƙarshen yaƙin Lebanon ɓangare ne na yarjejeniyar, yayin da Isra'ila ta bayyana cewa za ta ci gaba da kare kanta idan ta ga wata barazana.
Masana harkokin siyasa sun ce duk wani sabon tashin hankali tsakanin Isra'ila da ƙawayen Iran na iya rusa duk wani ci gaba da aka samu a tattaunawar.
2. Sake kaddamar da hari kan Iran
Rahoton Reuters ya nuna cewa ranar 28 ga watan Fabrairu, 2026 ne Amurka da Isra'ila suka kai hare-haren hadin gwiwa kan Iran, lamarin da ya yi sanadin mutuwar jagoran addinin kasar, Ayatollah Ali Khamenei.
Hakan ne ya tunzura Iran ta fara kai hare-haren ramuwar gayya kan Isra'ila da sansanonin sojin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya, wanda ya jawo yaki a tsakanin kasashen uku.
Iran ta sha nanata cewa tana son zaman lafiya domin ba ta taba fara kaddamar da yaki ba, amma ta ce a shirye take ta maida martani ga duk wanda ya takale ta domin kare martabarta.

Source: Getty Images
Ana ganin idan har Amurka da Isra'ila suka sake kai irin wadannan hare-hare adaidai lokacin da ake tsakiyar tattaunawar sulhu, hakan na iya wargaza yunkurin da ake na samar da zaman lafiya
3. Batun shirin nukiliyar Iran
Wani babban ƙalubale kuma shi ne makomar shirin nukiliyar Iran, wanda rahotanni sun nuna cewa kasar Musuluncin na da adadi mai yawa na sinadarin Uranium da aka sarrafa.
Tehran ta ci gaba da jaddada cewa shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne kuma ba ta da niyyar ƙera makaman nukiliya.
Sai dai har yanzu ba a cimma matsaya kan yadda za a kula da sinadaran da Iran ke da su ba, lamarin da zai kasance muhimmin batu a tattaunawar yarjejeniyar ƙarshe, kamar yadda The New York Times ta tattaro labarin.

Source: Getty Images
4. Mashigar ruwa ta Hormuz
Batun sake buɗe mashigar Hormuz, wacce Iran ta rufe tun a watan Fabrairun 2026, na daga cikin manyan ƙalubalen da ke gaban yarjejeniyar, kamar yadda AP News ta kawo.
Kafin rikicin ya ɓarke, kusan kashi 20 cikin 100 na mai da iskar gas na duniya na bi ta wannan mashiga ta Hormuz.
Yarjejeniyar ta tanadi sake buɗe hanyar ruwa bayan sanya hannu kan yarjejeniya ta ƙarshe, amma har yanzu akwai muhawara kan yadda za a tafiyar da ita da yiwuwar Iran ta sanya kuɗin harahin wucewa ga jiragen ruwa.
Masana sun ce cire nakiyoyin da aka dasa a Mashigar da dawo da cikakken tsaro na iya ɗaukar lokaci mai tsawo.

Source: Getty Images
Majalisa ta takawa Donald Trump birki
A wani rahoton, kun ji cewa Majalisar Amurka ta amince da wani kudiri da ke neman takaita ikon Shugaba Donald Trump kan ci gaba da amfani da sojoji a rikicin Iran.
Wannan ne karon farko da irin wannan kudiri ya samu nasarar wucewa a majalisun dokokin Amurka biyu, abin da ke nuna wani sabon kalubale ga Shugaba Trump.
Kudirin ya bukaci Shugaba Trump ya janye dakarun Amurka daga duk wani yaki ko rikici da Iran, sai dai idan majalisa ta ayyana yaki ko ta bayar da cikakken izini.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


