Yadda Cimma Yarjejeniya da Iran a Yaƙi Ya Kara Fito da Raunin Amurka a Fili

Yadda Cimma Yarjejeniya da Iran a Yaƙi Ya Kara Fito da Raunin Amurka a Fili

  • Shugaba Donald Trump yana shan suka bayan yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin Iran a yankin Gabas ta Tsakiya
  • Masu ruwa da tsaki na yankin Gulf sun fara nazarin sababbin hanyoyin hulɗa da Iran, yayin da yarjejeniyar ta taimaka wajen sake buɗe mashigar Hormuz
  • Duk da tsagaita wuta, har yanzu ana fuskantar rashin tabbas kan makomar shirin nukiliyar Iran, da kuma yiwuwar samar da cikakkiyar yarjejeniyar zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Masanin harkokin yau da kullum a duniya, Jeremy Bowen ya yi magana game da yakin Iran da Amurka.

Bowen ya bayyana cewa yaƙin da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar kan Iran ya zama babban kuskure na manufofin ƙasashen waje ga Shugaba Donald Trump.

Masana sun bayyana raunin Amurka a yaki da Iran
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Imam Mojtaba Khamenei, Donald J Trump.
Source: Facebook

Yayin zantawa da jaridar BBC, Bowen ya ce lamarin ya rage darajar Amurka a idon maƙiyanta musamman abin da ya shafi yarjejeniyar tsagaita wuta.

Kara karanta wannan

Sulhu tsakanin Iran da Amurka ya fusata Isra'ilawa, sun dura kan Netanyahu

Yakin Iran ya kawo matsala tsakanin ƙasashe

Bowen ya ce yaƙin ya jawo tangarɗa a dangantakar Amurka da wasu ƙasashen Larabawa masu arzikin mai a yankin Gulf.

Ana ganin gyaran wannan dangantaka zai buƙaci lokaci mai tsawo kafin komai ya dawo yadda yake.

A bayan fage, wasu ƙasashen yankin sun fara tattaunawa kan rage dogaro da Amurka tare da neman hanyoyin kyautata zamantakewa da Iran.

Ana sa ran yarjejeniyar da aka cimma za ta taimaka wajen dakatar da rikicin tare da rage wahalhalun da yaƙin ya jefa miliyoyin mutane. Haka kuma za ta ba da damar komawar harkokin kasuwanci yadda ya kamata.

Yadda yakin Iran ya fallasa raunin Amurka a duniya
Jagoran addinin Musulunci a Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Yadda bufe mashigar Hormuz zai yi tasiri

Rahoton ya nuna cewa sake buɗe mashigar Hormuz zai rage matsin lamba ga tattalin arzikin duniya saboda muhimmancinta wajen jigilar mai, gas da sauran kayayyakin da duniya ke buƙata.

Yaƙin ya haddasa mutuwar dubban mutane tare da lalata gidaje da wuraren kasuwanci, haka kuma, matsalar sufuri ta barazana ga samar da takin zamani da wasu kayayyakin noma.

Kara karanta wannan

Iran ta fara samun tagomashi daga Turai bayan tsayar da yaki da Amurka

Sai dai yarjejeniyar da aka cimma ba cikakkiyar yarjejeniyar zaman lafiya ba ce, abubuwa masu muhimmanci kamar makomar shirin nukiliyar Iran da sassauta takunkumai za su ci gaba da zama batutuwan tattaunawa.

Marubucin ya tuna cewa kafin yaƙin ya fara, Iran da Amurka suna gudanar da tattaunawa a Geneva kan shirin nukiliya.

Duk da haka, Amurka da Isra’ila sun ƙaddamar da hare-hare a ƙarshen watan Fabrairun 2026, shugabannin ƙasashen biyu sun yi hasashen cewa za su samu nasara cikin sauri kuma gwamnatin Tehran za ta durƙushe.

Akasin haka, hare-haren sun ƙarfafa haɗin kan shugabannin Iran, sababbin shugabanni da kwamandoji sun karɓi ragamar mulki cikin gaggawa tare da ƙara nuna tsayin daka.

Iran ta yi wa Isra'ila gagarumar barazana

Mun ba ku labarin cewa kasar Iran ta yi barazanar mayar da martani mai tsanani ga Isra'ila game da kai hare-haren a kudancin Lebanon.

Kasar Iran ta ce Isra'ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta da dama tun bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka.

Hare-haren Isra'ila a kudancin Lebanon sun kashe mutum hudu duk da yarjejeniyar da aka ce ta kawo karshen rikicin Gabas ta Tsakiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.