Gwamnatin Sakkwato Ta Yi Magana kan Rahoton da Ake Yadawa game da Bello Turji
- Gwamnatin jihar Sakkwato ta kwantar da hankulan jama'a kan rade-radin da ake yadawa cewa Bello Turji ya sayo sababbin makamai
- Rahotanni dai sun nuna cewa kasurgumin ɗan bindigan na kara shiri, inda aka ce 'yan Boko Haram na bai wa mayakansa horo
- Gwamnatin ta ce ta samar da motocin aiki, kayan sadarwa da tallafin kudi domin karfafa ayyukan jami’an tsaro a fadin jihar Sakkwato
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto, Nigeria - Gwamnatin jihar Sakkwato ta tabbatar wa al’umma cewa tana bibiyar duk wasu bayanan sirri da suka shafi tsaro, tare da daukar matakan kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Wannan na zuwa ne bayan rahotannin da ke yawo cewa fitaccen ‘dan bindiga, Bello Turji, ya mallaki sababbin makamai masu karfi tare da daukar wasu mayaƙan haya domin horas da mabiyansa.

Source: Facebook
Gwamnatin Sakkwato ta yi martani
Tribune Nigeria ta rahoto cewa mai ba Gwamna Ahmed Aliyu shawara kan harkokin tsaro, Kanal Ahmed Usman mai ritaya, ne ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai kan batun.
A cewarsa, hukumomin tsaro suna da masaniya kan abubuwan da ke faruwa a yankunan da ke fama da matsalar ‘yan bindiga, kuma suna daukar matakan dakile duk wata barazana.
Ya ce:
“Tsaro aiki ne da ba ya karewa, gwamnati na daukar duk wani rahoton sirri da muhimmanci.
"Muna aiki kafada da kafada da sojoji, ‘yan sanda, jami’an leken asiri da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa miyagun mutane ba su samu damar kawo cikas ga zaman lafiyar jihar ba.”
An yaba wa Gwamna Ahmed Aliyu
Ahmed Usman ya ce gwamnatin Gwamna Ahmed Aliyu ta nuna cikakken kuduri wajen inganta tsaro tun bayan hawanta mulki.
Ya bayyana cewa gwamnatin ta samar wa jami’an tsaro kayan aiki daban-daban da suka hada da motocin sintiri, babura, kayan sadarwa, man fetur da sauran muhimman kayayyaki domin saukaka ayyukansu.
“Gwamna Ahmed Aliyu ya nuna jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Tun bayan hawansa mulki, yake ba jami’an tsaro tallafin da suke bukata domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata," in ji shi.
Matakan da gwamnatin Sakkwato ta dauka
Hadimin gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatin Sakkwato ta amince da ware kudade masu yawa domin tallafawa ayyukan tsaro, tattara bayanan sirri da kuma shirye-shiryen tsaron al’umma.
Ya ce wadannan matakai sun kara karfin jami’an tsaro wajen mayar da martani cikin gaggawa ga duk wata matsalar tsaro, kamar yadda Leadership ta kawo.

Source: UGC
Ahmed Usman ya ce miyagun mutane kan yi amfani da farfaganda da yada jita-jita domin tsoratar da jama’a da rage musu kwarin gwiwa kan jami’an tsaro.
Ya ce gwamnati ba za ta raina kowace barazana ba, amma tana da yakinin cewa jami’an tsaro suna da kwarewa da shirin fuskantar duk wani kalubale.
Bello Turji ya ba gwamnati zabi 2
A wani labarin, kun ji cewa Bello Turji ya fito a wani bidiyo yana cewa sun kai hare-hare kan jami'an tsaro a yankunan Sokoto da Zamfara.
Kasurgumin dan ta'addan ya ce mayakan shi na shirye domin tattaunawa da hukuma, amma kuma zai cigaba da fafatawa da jami'an tsaro idan aka zabi yaki da shi.
Jagoran 'yan bindigan ya yi amfani da bidiyon wajen magana kan yiwuwar sulhu da hukumomi, inda ya nuna aniyarsa ta shiga tattaunawa idan gwamnati ta zabi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

