Iran Ta Yi Sabuwar Matsaya kan Hormuz bayan Gama Zama da Amurka
- Kasashen Qatar da Pakistan sun ce an samu fahimtar juna da aka yi tattaunawar kai tsaye tsakanin Amurka da Iran a ranar Lahadi
- Rahotanni sun nuna cewa an amince da wani tsari da za a bi wajen aiki tare domin cimma yarjejeniya ta ƙarshe cikin kwanaki 60 masu zuwa
- Iran ta amince da cigaba da bayar da damar cigaba da zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar Hormuz yayin da za a cigaba a tattaunawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Qatar da Pakistan sun sanar da samun gagarumin ci gaba a ƙoƙarin diflomasiyya da ake yi tsakanin Amurka da Iran bayan kammala zagaye na farko na tattaunawa a Switzerland.
Sun ce Amurka da Iran sun amince da wani tsarin aiki domin cimma yarjejeniya ta ƙarshe cikin kwanaki 60, tare da kafa wata “ƙungiyar daidaita rikice-rikice” domin tabbatar da kawo ƙarshen ayyukan soji a Lebanon.

Source: Getty Images
Matsaya kan mashigar Hormuz
Bayan fahimtar juna, Arab News ta wallafa cewa Iran da Amurka sun kafa wata “hanyar sadarwa kai tsaye” domin tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin aminci a mashigar Hormuz, kamar yadda suka bayyana.
“An gudanar da taron Lake Lucerne cikin yanayi mai kyau da fahimtar juna. An samu ci gaba, ciki har da ƙirƙirar wata hanya domin ci gaba da tattaunawa,”
In ji sanarwar haɗin gwiwar.
Sanarwar ta ce an kafa sabuwar hanyar sadarwar ne domin kauce wa afkuwar rikice-rikice da rashin fahimtar juna tare da tabbatar da zirga-zirgar jiragen kasuwanci cikin aminci ta mashigar Hormuz a cikin wa'adin kwanaki 60.
Bisa ga yarjejeniyar, Iran za ta yi iyakar ƙoƙarinta domin tabbatar da zirga-zirgar jiragen kasuwanci cikin aminci ba tare da karbar kudi ba.
Abubuwan da Iran da Amurka suka tattaunawa
Tawagogin Amurka da Iran, ƙarƙashin mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, da shugaban majalisar sokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, sun gudanar da zagaye na farko na tattaunawa kai tsaye na tsawon minti 100 a Burgenstock.
Al Jazeera ta wallafa cewa sun tattauna ne domin tattauna hanyoyin aiwatar da yarjejeniyar fahimtar Juna ta Islamabad da aka sanya wa hannu a ranar 17 ga Yunin 2026.
A cewar sanarwar, ɓangarorin sun amince da kafa wani babban kwamiti wanda zai kula da jagorancin siyasa na sasancin.
Kwamitin zai riƙa karɓar rahotanni daga manyan masu tattaunawar tare da sa ido kan ƙungiyoyin aiki na musamman da za su mayar da hankali kan shirin nukiliyar Iran.
Haka zalika za a lura da batutuwan takunkumi da hanyoyin warware rikice-rikice domin tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata.

Source: Getty Images
Haka kuma ɓangarorin sun amince da ƙirƙirar wata ƙungiyar daidaita rikice-rikice tsakanin su, Lebanon da kuma masu shiga tsakani domin tabbatar da mutunta yarjejeniyar dakatar da ayyukan soji a Lebanon.
An kashe sojojin Isra'ila 4
A wani labarin, mun kawo muku cewa kungiyar Hezbollah ta yi nasarar kashe wasu sojojin Isra'ila hudu da suka shiga wani yanki na Lebanon.
Kungiyar ta ce ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yakar dakarun Isra'ila da suka shiga yankunan Lebanon domin su yi mamaya a kasar.
Sanarwar da Hezbollah ta fitar ta nuna cewa ta yi wa sojojin Isra'ila da suke cikin wata tankar yaki kwanton bauna ne a lokacin da suke tafiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

