Ministan Buhari Ya Soki Sheikh Jingir da Ya Ji Kalaman Jagoran Kungiyar Izala
- Solomon Dalung ya maida wa Muhammad Sani Yahaya Jingir martani da ya yi wasu kalamai a garin Kano
- Malamin ya bukaci Musulmai su zabi tikitin Musulmi da Musulmi a 2027 domin nuna rinjayensu a Najeriya
- Dalung ya soki kalaman Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya ce zabe ba aikin nuna addinin da ya fi rinjaye ba ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Plateau - Solomon Dalung ya gagara yin shiru, ya tanka Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir a dalilin kalaman da ya yi.
Solomon Dalung ya tanka malamin Musuluncin ne bayan an ji shi a Kano yana daukar zafi wajen tallata tikitin Musulmi da Musulmi.

Source: Twitter
Solomon Dalung ya soki Sheikh Sani Jingir
A shafinsa na Facebook, tsohon ministan na harkokin matasa da wasanni ya soki matsayar malamin, yana cewa yana da hadari.
Sheikh Yahaya Jingir ya fito ya yi kira ga Musulmai su goyi bayan tazarcen Bola Tinubu da Kashim Shettima domin su nuna yawansu.
‘Dan siyasar ya ci gyaran dattijon, yake cewa samun Musulmi da Musulmi a fadar Aso Rock bai nufin talakan Musulmi zai ji dadi.
Solomon Dalung ya ce:
Amma a zahiri, tikitin Musulmi da Musulmi bai nufin iyalin Musulmai za su ci, su koshi. Bai kare Musulmin manomin da aka yi garkuwa da shi.
Bai kai ‘dan Musulmai makaranta mai kyau. Bai rage farashin man fetur, abinci ko magani. Bai samar da ayyukan yi. Bai gyara rubabben titi ko ya samar da lantarki.
A sakon shi da yake yawo har a kafar X, Solomon Dalung ya yi tir da kalaman da Jingir yake yi game da wadanda ba Musulmai ba.
Yadda Dalung ya kare Musulmai da Kiristoci
Dalung ya tuna wa malamin cewa kiristoci makwabtansa ne wadanda suke biyan haraji domin a iya tafiyar da harkokin gwamnati.
Ya ce:
Kiristocin da ke zaben musulman ‘yan takara? Musulman da ke watsi da siyasar addini?
Miliyoyin ‘yan Najeriya da kawai suke son ganin shugabanci na gari ba tare da la’akari da addinin ‘dan takaran ba?

Kara karanta wannan
Bincike ya zo ƙarshe, an ji dalilin Kanal Mohammed Ma'aji na shirya yi wa Tinubu juyin mulki
Tsohon ‘dan takaran gwamnan na Filato yake cewa addini ba fagen daga ba ne da ake nuna addinin da yake yin galaba a kan wani.
Duk da haka, Dalung Esq ya ce babu matsala idan aka goyi bayan tikitin Muslim-Muslim idan da adalci ko akwai cancanta.
"Amma idan lamarin ya koma ‘mun fi ku yawa, saboda haka za mu mamaye ku’, to mun rabu da damukaradiyya zuwa lissafin siyasa."
- Solomon Dalung
A karshe ya ce Najeriya ta Musulmai da Kiristoci ne har da wadanda ba su da addini.
Ya bada shawarar a dage wajen ganin gwamnati ta maida hankali wajen samar da tsaro, ayyukan yi, abinci, asibitoci da makarantu.
Shehin Darika bai goyon bayan Muslim-Muslim
Ganin addinan Musulunci da Kiristanci duka suna da mabiya sosai a Kaduna, an rahoto Sheikh Haliru Maraya ya soki tikitin Musulmi da Musulmi.
Shehin malamin darikar na Tijjaniya ya sake sukar tsaida Musulmi da Musulmi takarar gwamnan Kaduna, yana mai cewa hakan ba adalci ba ne.
Sheikh Haliru Maraya ya yi aiki da gwamnatocin Namadi Sambo da Ramalan Yero wadanda duk suka jawo kiristoci a matsayin mataimaka da suke ofis.
Asali: Legit.ng
