
Labaran kasashen waje







An samu asarar rayukan aƙalla mutum takwas bayan wani jirgin sama na yaƙi na ƙasar Kenya wanda yake ɗauke da sojoji ya yi hatsari. An fara gudanar da bincike.

Kasar China ta rage yawan bashin da ta ke bai wa Najeriya da sauran kasashen Nahiyar Afirka kan saba ka'idar biyan bashi kan lokaci kamar yadda aka yi alkawari.

Shugaban kamfanin X da aka fi sani da Twitter, Elon Musk ya ce masu amfani da manhajar za su fara biyan kudi duk wata don rage amfani da shafukan bogi.

Rahoto ya bayyana cewa, sojoji sun kwace mulki a kasar Kongo da ke tsakiyar Afrika. An bayyana gaskiyar abin da ke faruwa a kasar da shugaban mai dogon zamani.

Ministan harkar wuta ya fito ya yi dogon bayani a game da durkushewar babban layin lantarki, Adebayo Adelabu ya ce matsala ce aka samu, hakan ya yi sanadiyyar cikas.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhininsa bisa ibtila'in ambaliyar ruwan da ya afkawa ƙasar Libya, wacce ta yi sanadin rasuwar sama da mutane 6,000.

Wata mata ƴar ƙasar Kenya wacce ke rayuwa a kusa da rafin Baringo ta bayyana yadda kada ta raba ta da ƙafarta guda ɗaya. Ta ce rayuwa ta koma mai wuya a gareta.

A wani salo da ba a saba gani ba, kasar Faransa na rokon Morocco da ta yi hakuri ta karbi tallafin Yuro miliyan biyar da ta yi niyyar ba ta bayan girgizar kasa.

Lambar Godwin Emefiele ta fito a wani bincike da ake yi, nan da ‘yan kwanaki kadan mutanen Najeriya su ji labarin badakalar da za ta shiga cikin mafi girma a tarihi.
Labaran kasashen waje
Samu kari