Kwankwaso Ya Tuna Abin da Pantami Ya Yi Masa a Baya, Ya Tabo Wakar Rarara
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce Dauda Kahutu Rarara ya dade yana sukar ’yan siyasa, bai kamata Farfesa Isa Ali Pantami ya fusata ba
- Kwankwaso ya ce Pantami ya bar malanta ya shiga siyasa, don haka bai kamata ya rika tsammanin za a keɓe shi daga sukar ’yan siyasa ba
- Tsohon gwamnan Kano ya bayyana cewa Rarara ya taba zagin sa, Abdullahi Ganduje da da Ibrahim Shekarau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sanata Rabiu Musa ya yi martani game da wakar da aka ce Dauda Kahutu Rarara ya ci mutuncin Farfesa Isa Ali Pantami.
Tsohon gwamnan Kano ya dura kan Pantami duba da cewa ya shiga siyasa bai kamata ya rika amfani da rigar malanta ba.

Source: Facebook
Kwankwaso ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo yayin hira da shafin DCL Hausa a yau Talata 11 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan
2027: Babban jigon APC a Arewa ya tada rigima, ya ce ba zai sake tallata Tinubu ba
A cikin bidiyon, Kwankwaso ya ce kafin Rarara ya zagi Pantami, ya zagi mutane da dama musamman yan jihar Kano.
Sanata Kwankwaso ya ce Rarara ya zage shi, ya zagi Ganduje da kuma Shekarau domin haka bai kamata shi Pantami ya ji haushi ba.
Ya ce:
"Kafin Rarara ya zagi Pantami ai ni ya fara zagi, ya zagi Ganduje ya zagi Shekarau, ya zagi mutane da yawa a Kano.
"Mu da ya ke yan siyasa ne, ai ka ga mun tafiyar da abin yadda ya kamata amma shi ne nake cewa ba za ka baro malanta ka zo ka shigo siyasa kuma ka ce abin da ake yi wa malamai kai ma shi za a yi maka.
"Abin da ya yi masa yanzu, so min tabi ne, shi malam Pantami menene bai fada a kai na ba, yaranmu har tare shi suka a Kano za su kwankwashe shi ai."

Source: Facebook
Darajar da Pantami ya samu ta malanta
Kwankwaso ya ce darajar malanta ya saka yan Kwankwaso ba su kwankwashe shi lokacin da ya zage shi saboda ya shiga siyasa amma yana zagin yan siyasa a kan mimbari.
"Wannan darajar malanta ta sa aka kyale shi, a lokacin ma ya ce ya dade yana siyasa, ashe dan siyasa ne ya hau mimbari yake zagin yan siyasa.
"Yanzu wannan malami, Allah cikin ikonsa, duk jam'iyyun nan ba wacce ya zaga sai PDP amma ka ga ya zaga ya zago ya zo ya shige ta, zagin da ya yi mata alkafira amma yanzu yana cikinta alkafira."
- Rabiu Musa Kwankwaso
Rarara: PDP ta soki wakarsa kan Pantami
Mun ba ku rahoto cewa jam'iyyar PDP a Gombe ta ce wakar Dauda Kahutu Rarara da ta ambaci Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami na dauke da batanci da rashin mutuntawa.
PDP ta zargi mawakin da kokarin bata sunan dan takararta na gwamna tare da cewa sabanin siyasa bai kamata ya zama hanyar cin mutuncin mutane ba.
Jam'iyyar ta bukaci 'yan siyasa da magoya bayansu su mayar da hankali kan manufofi da shirye-shirye gabanin zaben 2027 maimakon zage-zage.
Asali: Legit.ng
