'Yan Sanda Sun Cafke Fasto da Sojoji kan Shirya Sace Matan Manyan Malaman Addini a Plateau

'Yan Sanda Sun Cafke Fasto da Sojoji kan Shirya Sace Matan Manyan Malaman Addini a Plateau

  • Rundunar ’yan sandan Jihar Plateau ta kama wani fasto da jami’an tsaro biyu kan zargin shirya satar matan manyan limamai biyu a Jos
  • An kama wadanda ake zargin ne bayan ’yan sanda sun samu sahihan bayanan sirri kan wata makarkashiyar aikata laifi da yunkurin satar mutane da aka dakile
  • ’Yan sanda sun ce daya daga cikin wadanda ake zargin ya amsa cewa yana da hannu a laifin yayin gudanar da bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jos, Plateau - Rundunar ’yan sandan Jihar Plateau ta sanar da kama wani fasto da jami’an tsaro biyu bisa zargin hada baki domin yin garkuwa da matan manyan bishops biyu a Jos.

Majiyoyi a rundunar ’yan sandan jihar sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 2:10 na rana a ranar 7 ga watan Agusta, 2026.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji da yan sanda sun rutsa yan bindiga fiye da 200 ta sama da ƙasa

An cafke fasto a jihar Plateau
'Yan sanda sun kama fasto a Plateau Hoto: Legit.ng
Source: Original

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Rundunar ta bayyana daya daga cikin wadanda ake zargin da sunan Rev. Hassan Yunisim Mijah, mai shekaru 42, mazaunin Tudun Wada da ke Jos ta Arewa.

An zargi jami’ai uku da makarkashiya

A cewar ’yan sandan, ana zargin Mijah da hada baki da Sgt. Ezra Sunday, jami’in Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, da OS Usman Khalid, jami’in Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya. Jami’an biyu na aiki ne a Sector 1 na Operation Enduring Peace(OPEP), Jos.

Rundunar ta ce wadanda ake zargin sun shirya yin garkuwa da matan Bishop Ephraim Gongden da tsohon Bishop Benjamin Kwashi.

Rahotanni sun ce limaman biyu mazauna yankin Rantya ne da ke Karamar Hukumar Jos ta Kudu.

Yadda aka kama wadanda ake zargin

Rundunar ta ce bayan samun bayanan sirrin, jami’an ’yan sanda karkashin jagorancin kwamandan Violent and Criminal Response Unit (VCRU) suka fara wani samame nan take.

Kara karanta wannan

Bincike ya zo ƙarshe, an ji dalilin Kanal Mohammed Ma'aji na shirya yi wa Tinubu juyin mulki

Samamen ya kai ga kama mutanen uku da ake zargi da hannu a makarkashiyar da aka shirya ta sace matan manyan limaman na coci.

“Bayan an yi musu tambayoyi, wadanda ake zargin sun amsa aikata laifin,” in ji rundunar ’yan sandan.

Rundunar ta kuma ce an sanar da Operation Enduring Peace (OPEP) a hukumance game da kama jami’an tsaron biyu da ke aiki a karkashin rundunar.

Bincike na ci gaba da gudana

Hukumomin ’yan sanda sun ce bincike na ci gaba da gudana domin gano cikakken bayani kan makarkashiyar da ake zargin an shirya.

Haka kuma, ’yan sandan na kokarin gano tare da kama sauran mutanen da ake zargin suna cikin wannan kungiyar masu aikata laifuka.

Yan sanda a Plateau sun kama wani limamin coci da jami’an tsaro biyu bisa zargin shirya sace matan wasu fitattun bishops biyu a Jos.

'Yan sanda sun kama fasto a Plateau
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar 'yan sandan jihar Sokoto sun dakile wani hari da 'yan bindiga suka kai a jihar Sokoto.

Jami'an 'yan sandan sun kuma ceto tumaki 43 da 'yan bindiga suka sace daga kauyen Anada da ke karamar hukumar Binji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng