Jagorori Sun Hadu a Masar bayan an Gano Ƙaruwar Ƙin Musulmi a Duniya
- Ƙasashen duniya sun bayyana matakin da ya dace a dauka game da karuwar kin jinin Musulmi na ba gaira ba dalili da ake fama da shi a sassa da dama
- Wani bincike ya nuna cewa kusan kashi biyu cikin uku na Musulman Amurka suna fuskantar kyama saboda kawai su mabiya addinin Musulunci ne
- Taron da aka gudanar a Masa ya ƙaddamar da sabon dandalin haɗin gwiwa na ƙasa da ƙasa domin yaƙi da nuna wariya da kin jinin Musulmi a duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Egypt – Jagorori da masu ruwa da tsak da ke yaƙi da nuna wariya ga addinin Musulunci da Musulmi sun sake zama karo na biyu a kasar Masar.
A wannan taro, an yi kira da a ƙara haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe da ƙungiyoyin duniya domin dakile ƙarin yawaitar kin jinin mabiya addinin Islama.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta kawo labarin cewa an mayar da shawarwarin da aka cimma zuwa shirye-shiryen da za su inganta tattaunawa, haƙuri da zaman lafiya.
An yi taron Musulmi a Masar
Anadolu Ajansi ta kawo labarin cewa an gudanar da taron na kwanaki biyu a hedikwatar Ƙungiyar Kasashen Larabawa da ke birnin Alƙahira na ƙasar Masar.
Ƙungiyar Kasashen Larabawa da Hukumar Ilimi, Kimiyya da Al'adu ta Duniyar Musulmi (ICESCO) ne suka shirya taron saboda karuwar tsana da ake nunawa Musulmi.
Taron ya haɗa jami'an gwamnatoci, ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, shugabannin addinai, ƙungiyoyin fararen hula da wakilan matasa ƙarƙashin taken: "Al'ummomin Musulmi a ƙasashen Yamma da rawar da suke takawa wajen yaƙi da kin jinin Musulmi."
Mataimakin babban sakataren Ƙungiyar Kasashen Larabawa mai kula da harkokin sa ido, Ambasada Hussein Hindawi, ya ce 'yancin addini da akida na daga cikin haƙƙoƙin ɗan Adam da yarjejeniyoyin ƙasa da ƙasa suka tanada.
An yi gargadi kan kyamar Musulmi
Ambasada Hussein Hindawi ya yi gargadin cewa tsanar da ake yi wa Musulmi a duniya ya fara wuce daidaikun mutane, ya zama gagarumar matsala a duniya.
Ya ce bayanan Hukumar Tarayyar Turai mai kula da haƙƙoƙin ɗan Adam sun nuna cewa kashi 47 cikin 100 na Musulmai a ƙasashe 13 na Tarayyar Turai sun fuskanci nuna wariyar launin fata a shekarar 2024.

Source: Facebook
Idan aka kwatanta wannan adadi da na shekarar 2016, za a ga an samu kari, domin a wancan lokai akalla kashi 39 cikin 100 ne suka fuskanci matsalar.
A cewarsa, kashi 39 cikin 100 sun fuskanci wariya wajen neman aiki, kashi 27 cikin 100 sun gamu da cin zarafi na wariyar launin fata, yayin da kashi huɗu cikin 100 suka fuskanci hare-hare.
Ya kara da cewa a cikin dukkanin wadannan mutane da aka ci zarafin su, kashi shida cikin 100 ne kawai suka kai irin waɗannan ƙorafe-ƙorafen ga hukumomi.
Hindawi ya ce alaƙanta Musulmi da ta'addanci, aikata laifuka da ƙaura ba bisa ƙa'ida ba na ƙara ruruta ƙiyayya, saboda haka ya buƙaci gwamnatoci, cibiyoyin addini, makarantu, kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin fararen hula su haɗa hannu wajen yaƙi da kalaman ƙiyayya.
Kiristoci sun fi Musulmi more gwamnatinTinubu
A wani labarin, kun ji cewa 'kungiyar matasan Musulmi ta NACOMYO ta yi yi karin haske game da korafin da ake kan tikitin Musulmi da Musulmi a Najeriya da yadda ake cin moriyar gwamnati.
Kungiyar ta kare tsarin takarar Musulmi da Musulmi na Bola Tinubu, tana mai cewa adawar wasu Kirista kafin zaben 2027 munafunci ne domin su ne a gaba-gaba wajen samun amfanin da romon gwamnati.
Kungiyar ta NACOMYO ta bukaci kungiyoyin addini su ci gaba da bai wa gwamnati shawara da addu’a domin ci gaban Najeriya tare da fatan a samu rayuwa mai cike da jin dadi da walwala maimakon korafi.
Asali: Legit.ng


