Mahaddatan Kur'ani za Su Samu Naira Biliyan 3.7 a Gasar da ake a Saudi

Mahaddatan Kur'ani za Su Samu Naira Biliyan 3.7 a Gasar da ake a Saudi

  • Masu fafatawa 334 daga ƙasashe 133 ne suka shiga gasar hadda, karatu da fahimtar Alƙur’ani mai girma da ake gudanarwa a birnin Makkah na Saudiyya
  • Gasar ta bana ta samu mafi yawan mahalarta tun bayan fara gudanar da ita, yayin da jimillar kuɗin kyaututtukan gasar ta kai Riyal miliyan 10.26, kwatankwacin Naira biliyan 3.7
  • A karon farko, an ware gasar mata daban da za a gudanar a Makkah, yayin da za a gudanar da zaman ƙarshe na maza da bikin rufe gasar a Masallacin Harami

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Makkah – An fara zama karo na 46 na gasar Sarki Abdulaziz ta ƙasa da ƙasa ta hadda, karatu da fassarar Alƙur’ani mai girma a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya ranar Alhamis.

Gasar, wadda ake gudanar da ita ƙarƙashin kulawar Mai Kula da Masallatai Biyu Masu Tsarki, Sarki Salman bin Abdulaziz, ta samu mahalarta 334 maza da mata daga ƙasashe 133 na duniya.

Kara karanta wannan

Halin da wasu ƴan Najeriya ke ciki a gidan gyaran hali na Saudiyya

Wajen gasar karatun Kur'ani
Yadda aka kaddamar da gasar karatun Kur'ani a Saudiyya. Hoto: SPA
Source: Facebook

Saudi Gazette ta ruwaito cewa Ma’aikatar Harkokin Addinin Musulunci ta Saudiyya ce ta shirya gasar, wadda za ta ci gaba har zuwa ranar 6 ga watan Rabi’ul Awwal, da ta yi daidai da 19 ga watan Agustan 2026.

Gasar na da nufin ƙarfafa matasan Musulmi wajen haddace Alƙur’ani, fahimtar ma’anoninsa da yin tunani a kan koyarwarsa, tare da haɓaka gasa tsakanin mahalarta.

An ware gasar mata daban

A wani sabon tarihi, an ware gasar mata daban da za a gudanar a Makkah, yayin da zaman ƙarshe na rukunin maza da bikin rufe gasar za a gudanar da su a Masallacin Harami.

Daily Trust ta wallafa cewa gasar ta ƙunshi rukuni biyar, inda jimillar kuɗin kyaututtukan da aka ware ya kai Riyal miliyan 10.2, kwatankwacin Naira biliyan 3.7.

Adadin kuɗin kyautar shi ne mafi girma da aka taɓa warewa tun bayan ƙaddamar da gasar, lamarin da ya ƙara mata muhimmanci a tsakanin gasa na Alƙur’ani da ake gudanarwa a duniya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fadi yadda ake kashe tulin bashi da ake laftowa Najeriya

Dalilin gudanar da gasar

Masu shirya gasar sun bayyana cewa manufarta ita ce karfafa matasa Musulmi su haddace Alƙur’ani, su fahimce shi kuma su yi tunani a kan koyarwarsa.

Haka kuma, tana ƙoƙarin ƙarfafa gasa mai kyau tsakanin masu haddar Alƙur’ani tare da nuna irin ƙoƙarin da Saudiyya ke yi wajen hidima ga Alƙur’ani da girmama waɗanda suka haddace shi.

Littafin Allah mai tsarki
Hoton Al-Kur'ani an bude ana karatu. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Saudi ta yi yarjejeniyar tsaro

A wani labarin, mun ruwaito cewa Saudiyya, Turkiyya da Pakistan sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro ta haɗin gwiwa a Makkah, wadda ta kafa tsarin kare juna tsakanin ƙasashen uku.

Yarjejeniyar ta tanadi cewa duk wani hari na makami da aka kai wa ɗaya daga cikin ƙasashen uku za a ɗauke shi a matsayin hari da aka kai wa sauran ƙasashen biyu.

Yarjejeniyar ta kuma ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Saudiyya, Turkiyya da Pakistan, bisa dogaro da dangantakarsu ta tarihi, haɗin kan Musulunci da muradun tsaro da suka yi tarayya a kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng