Trump Ya Fadi Sunayen Masu Safarar Kudin Ta'addanci a Najeriya, Kasashe

Trump Ya Fadi Sunayen Masu Safarar Kudin Ta'addanci a Najeriya, Kasashe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Amurka ta fitar da sunayen mutane da kamfanonin da ake zargi da hannu a hanyoyin samar da kuɗi ga ƙungiyar ISIS.

Sanarwar da Amurka ta fitar a ranar Litinin ta shafi maza uku da kamfanoni shida waɗanda ta ce sun taimaka wa ISIS wajen jigilar kuɗi tsakanin ƙasashe.

Kara karanta wannan

Yadda aka nemi ceto malamar Islamiyya amma mutane suka taru suka kashe ta

Shugaba Donald Trump
Danald Trump yayin wani jawabi a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton da ma'aikatar kudi ta Amurka ta fitar a yanar gizo ya nuna cewa ana zargin mutanen suna gudanar da ayyukansu ne a Turai, Gabas ta Tsakiya da Afirka ta Yamma ciki har da Najeriya.

Waye dan Najeriya da aka ambata?

Daga cikin waɗanda aka sanya wa takunkumi akwai wani ɗan Najeriya wanda ake zargin kamfanoninsa na canjin kuɗi sun kasance hanyoyin da ake amfani da su wajen gudanar da harkokin kuɗin ISIS.

An bayyana ɗan Najeriyan a matsayin Muhammad Mukhtar Adamu, wanda ake dangantawa da ISIS a Yammacin Afirka.

Daily Post ta wallafa cewa an haife shi a ranar 2 ko 3 ga Agusta, 1990, kuma an nuna cewa yana zaune ne a yankin Agege da ke Legas.

Ɗan Siriyan shi ne Abdelhakim Boukich, wanda aka fi sani da Babili Muhammad, an haife shi a ranar 15 ga Disamba, 1993, ko kuma 1 ga Janairu, 1991.

Kara karanta wannan

An shigar da korafi wajen INEC domin neman hana Tinubu takarar 2027

Ɗan Faransan kuwa shi ne Abderrahmane Miloud, wanda aka fi sani da Ghazi Ibrahim, an haife shi a watan Agustan 1992. Dukkaninsu ana danganta su da ƙungiyar ISIS.

Shugaban Najeriya da sojojin Amurka
Shugaba Bola Tinubu da sojojin Amurka a Aso Villa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Kamfanonin da aka zarga

Kamfanoni uku da ake dangantawa da Muhammad, kuma suke da hedikwata a Najeriya, sun haɗa da General Currency Bureau De Change Limited da ke Legas, wanda aka kafa a ranar 9 ga Janairu, 2019.

Sauran kamfanonin sun haɗa da Manhattan Bureau De Change da ke kan titin Murtala Muhammad a Kano, wanda aka kafa a ranar 26 ga Janairu, 2021.

Sai kuma Nine To Nine Exchange Bureau De Change da ke cikin harabar FAAN a titin filin jirgin sama na Legas, wanda aka kafa a ranar 22 ga Agusta, 2017.

Amurka za ta yi ciniki da Iran

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin shugaba Donald Trump ta shirya yadda za a yi amfani da kudin Iran da za a mika bayan sulhu.

A wani bayani da ya yi, Trump ya sanar da cewa za a yi amfani da kudin ne wajen sayen kayan abinci daga wajen manoman Amurka.

Sai dai kasar Iran ta mayar masa da martani da cewa wannan ba ya cikin sharadin da suka yi kuma hakan ba zai taba yiwuwa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng