Wuta Ta Yi Wuta: Babban Sojan Amurka na Neman a Fita a Yaki da Iran
- Babban hafsan sojin Amurka, Janar Dan Caine, ya fara neman hanyar fita daga yaƙin da ƙasar ke yi da Iran saboda ƙarin hare-hare na iya jefa Amurka cikin matsala
- Majiyoyi sun ce Caine ya tattauna damuwarsa da wasu manyan jami'an gwamnatin Donald Trump, ciki har da John Ratcliffe da Marco Rubio
- Janar Caine na ganin hare-haren sama kaɗai ba za su iya cimma burin Trump ba, yayin da shugaban Amurka ya nuna rashin sha'awar tura sojojin ƙasa zuwa Iran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington, D.C. – Babban hafsan sojin Amurka, Janar Dan Caine, na neman wata hanyar da za ta ba Amurka damar fita daga yaƙin da take yi da Iran, yayin da zaɓuɓɓukan da ake da su na ƙara tsananta rikicin ke fuskantar ƙalubale.
Majiyoyi uku da suka san halin da ake ciki sun bayyana cewa Caine ya yi imanin cewa wasu matakan soji na iya jefa Amurka cikin ƙarin matsala, yayin da hare-haren sama kaɗai ba za su iya cimma manufofin da Shugaba Donald Trump ya bayyana ba.

Source: Getty Images
CNN ta rahoto cewa ɗaya daga cikin majiyoyin ya bayyana matsayar babban hafsan a takaice da cewa, "Caine na neman mafita."
Maganar da Janar Caine ya yi
Majiyoyin sun ce na Janar Caine kaɗai ne ke ganin cewa yaƙin ya kai wani yanayi da ya kamata a dauki mataki mai muhimmanci ba.
An ce ya tattauna damuwarsa kan ƙara tsananta yaƙin da wasu manyan jami'an gwamnatin Trump, ciki har da Daraktan CIA John Ratcliffe, Ministan Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio da Mataimakin Shugaban Ƙasa JD Vance.
A cewar majiyoyin, Caine ya kuma gudanar da wasu tattaunawa ta gefe da jami'an da ke da irin wannan ra'ayi domin daidaita matsayar hukumomin gwamnati kafin ganawa da shugaban ƙasa.
Dalilin neman fita a yaƙin
Majiyoyin sun ce babban hafsan yana ƙoƙarin bayyana wa sauran jami'an gwamnatin Trump iyakoki da haɗuran da ke tattare da zaɓuɓɓukan soji da ake da su, har da waɗanda ba sa buƙatar tura sojojin Amurka ta ƙasa.
Ɗaya daga cikin majiyoyin ta ce wannan matakin na iya kasancewa wani yunƙuri ne na Caine na kare sojojin Amurka daga shiga cikin wani yaƙi mai tsawo da sakamakonsa ba shi da tabbas.

Source: Facebook
Trump dai ya sha nuna cewa ba ya son tura sojojin ƙasa zuwa Iran, inda yake nuna cewa hare-haren sama za su iya tilasta wa Tehran amincewa da yarjejeniyar da ta dace da sharudan Amurka.
Roya News ta ce Caine da wasu jami'an gwamnatin Trump na ganin cewa da wahala a cimma wannan sakamakon ta hanyar hare-haren sama kaɗai.
Maganar fadar White House
Da aka nemi karin bayani, kakakin Caine, Joseph Holstead, ya ce ba sa magana kan tattaunawar sirri da babban hafsan ke yi da shugaban ƙasa, ministan tsaro ko wasu manyan jami'ai.
Fadar White House kuwa ta yaba da rawar da Caine ke takawa a tsaron ƙasa, tana mai cewa nasarar ayyukan soji da dama da Amurka ta gudanar ta isa ta nuna irin gudunmawarsa.
Saudi ta kulla yarjejeniyar tsaro
A wani labarin, mun ruwaito cewa Saudiyya, Turkiyya da Pakistan sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar tsaro ta bai ɗaya, inda suka amince cewa hari kan ɗaya daga cikin ƙasashen zai zama kamar hari ne kan dukkaninsu.
An sanar da yarjejeniyar ne yayin wata ganawa tsakanin Yariman Saudiyya Mohammed bin Salman, Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif a birnin Makka.
Matakin ya biyo bayan hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai wa Iran, wanda ya haifar da martani daga Tehran da kawayenta tare da kawo cikas ga zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz da Bahar Maliya.
Asali: Legit.ng


