Asiri Ya Tonu: Isra'ila na Amfani da Farin Sinadari Mai Guba a Lebanon
- Rundunar sojin Isra’ila ta yi amfani da wani sinadari mai guba wanda zai iya yin matuƙar illa a wuraren da jama’a ke zaune a kasar Lebanon
- An ga hayaki na musamman da ke fitowa daga irin wannan makami har zuwa ranar 30 ga Mayun 2026 a Nabatieh, wani birni mai mutane 40,000
- Sauran bidiyoyin da aka tabbatar da sahihancinsu sun nuna cewa an yi amfani da sinadarin a kusa da birnin Tyre da ke bakin teku da wasu garuruwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Israel - Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun ce sun tattara hujjoji da ke nuna cewa Isra’ila ta yi amfani da sinadarin phosphorus a kan yankunan fararen hula a Lebanon.
An bayyana phosphorus a matsayin wani irin sinadari da zai iya haddasa mummunar ƙuna, matsalolin numfashi da mutuwa ga dan Adam.

Kara karanta wannan
Bayan an ja kunnen Netanyahu, Iran ta kai harin makamai masu linzami zuwa Isra'ila

Source: Getty Images
New York Times ta ruwaito cewa Isra’ila ta yi amfani da sinadarin a garin Nabatieh a ranar 30 ga Mayun 2026 bayan ta tabbatar da sahihancin bidiyoyin kafafen sada zumunta.
Zargin da aka yi wa Isra'ila
Rahotanni sun nuna cewa an dade ana zargin Isra’ila da amfani da sinadarin ta hanyar da ke jefa fararen hula cikin haɗari kafin tabbatar da ta yi amfani da shi a Lebanon.
Ba a haramta shi a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa ba, amma haramun ne amfani da sinadarin a cikin ko kusa da wuraren da jama’a ke zaune saboda yana iya haddasa babbar illa.
“Yana iya haddasa munanan raunuka — raunukan da za su kasance har abada,”
“Ko kuma ya haddasa mutuwa.”
In ji mai bincike kan Lebanon a ƙungiyar HRW, Ramzi Kaiss
Menene sinadarin phosphorus?
Kungiyar HRW ta wallafa cewa sinadarin yana da kauri kamar tikar zuma kuma yana kamawa da wuta nan take idan ya haɗu da iskar da ake shaka.

Kara karanta wannan
Isra'ila ta yi ikirarin hallaka kwamandan Hezbollah ana kokarin tsagaita wuta a Lebanon
Yarjejeniyar hana aiki makaman masu sinadarai ta ayyana phosphorus a matsayin sinadari mai saka jikin mutum ya kone sosai.
Ƙasashe na iya amfani da sinadarin domin samar da hayakin kariya, kuma rundunar tsaron Isra’ila ta ce saboda wannan dalili take amfani da shi a wasu harsasanta na manyan bindigogi.
Sai dai yarjejeniyar makamai ta haramta amfani da irin waɗannan sinadarai a yankunan fararen hula, kuma wannan shi ne abin da HRW da Amnesty International suke zargin Isra’ila da aikatawa.

Source: Getty Images
Meyasa sinadarin ke da hadari?
Sinadarin na iya jawo barnar da ba a iya ganewa a cewar masana. A cewar Human Rights Watch, harsashin babban bindiga guda ɗaya mai ɗauke da shi na iya yaɗa sinadarin a faɗin yankuna da dama.
Da zarar ya faɗi ƙasa, sinadarin yana manne wa fata da tufafi. Yana iya haddasa mummunan ƙuna da ke shiga har cikin ƙasusuwa, tare da samar da ƙwayoyin da ke lalata idanu da hanyoyin numfashi.
Isra’ila ta kai hari Iran
A wani rahoton, mun kawo muku cewa Isra’ila ta kaddamar da hare-haren sama da sanyin safiyar Litinin kan wasu wurare Iran.
Tashar talabijin ta gwamnatin Iran ta ruwaito an ji karar fashewa a Isfahan, Karaj, Tabriz da Tehran, ba tare da yin ƙarin bayani ba.
Iran ta rufe sararin samaniyar da ke kewaye da Filin Jirgin Sama na Imam Khomeini da ke Tehran bayan harin da Isra’ila ta kai.
Asali: Legit.ng
