Labaran Duniya
Watan Disamba na dauke da bukukuwa daban-daban, daga Kirsimeti da ranar dambe zuwa daren sabuwar shekara. Mutane na sada zumunci, da tuno da al'adun gargajiya.
Kasar Chadi ta sanar da yanke alakar soji da Faransa. A yanzu haka ƙasar Chadi ta karkara wajen kulla alaka da Rasha. Sojojin Faransa za su fice daga kasar Chadi.
Kungiyar cinikayya ta duniya watau WTO ta sake naɗa tsohuwar ministar kuɗi a Najeriya, Drm Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin Darakta Janar karo na biyu.
Mai kuɗin duniya na bakwai Warren Buffett ya yi kyautar $1.1b kudin da ya haura Naira tiriliyan daya. Warren Buffett ya ce ya san mutuwa na daf da isowa gare shi.
Kungiyar tattara bayanan gwaninta watau GWR ta tabbatar da mutuwar mutumin da ya fi kowa tsufa a duniya, John Tinniswood, yana da shekara 112 da haihuwa.
Isra'ila za ta tsagaita wuta a Lebanon a yakin da ta ke da ƙungiyar Hisbullah. Amurka ce ta shiga tsakanin Isra'ila da yan Hisbullah domin kawo karshen rikicin.
Yan sandan kasar Finland ta kama shugaban yan ta'addar Biyafara, Simon Ekpa. An kama Simon Ekpa ne saboda ingiza mutane su yi ta'addanci a Kudancin Najeriya.
Shugaban kasar Paraguay ya kamu da rashin lafiya ana taron da Bola Tinubu ya halarta a kasar Brazil. Shugaban kasa Santiago Pena na karbar magani a asibiti.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce Najeriya ta amince ta shiga sabuwar kungiyar kawancen kasashen duniya saboda cimma burinta na kawar da yunwa da talauci.
Labaran Duniya
Samu kari