Abin da Muka Sani kan Yarjejeniyar da Amurka da Iran Za Su Iya Kullawa don Kawo Karshen Yaki

Abin da Muka Sani kan Yarjejeniyar da Amurka da Iran Za Su Iya Kullawa don Kawo Karshen Yaki

  • Alamu sun nuna cewa Amurka da Iran na shirin rattaba hannu kan yarjejeniyar da za ta kai ga kawo karshen yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya
  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa yarjejeniyar da za a kulla za ta hana Iran mallakar makamin nukiliya ta kowace hanya
  • Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, yarjejeniyar za ta sanya a dage killace tashoshin jiragen kasar da Amurka ke yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran na shirin kulla yarjejeniya domin kawo karshen yaki.

Shugaba Donald Trump na Amurka, ya nuna cewa za a iya rattaba hannu kan yarjejeniyar a ranar Lahadi, 14 ga watan Yunin 2026.

Trump ya yi magana kan yarjejeniyar Amurka da Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, a Oval Office Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shugaba Trump ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Truth Social a ranar Asabar, 14 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Trump ya ballo ruwa, 'yan majalisa sun bude masa wuta kan shirin yarjejeniya da Iran

Me Donald Trump ya ce kan yarjejeniyar?

Donald Trump ya siffanta yarjejeniyar da aka yi da Iran a matsayin “katanga ta hana samun makamin nukiliya".

Shugaban kasar na Amurka ya kuma ya ce Iran za ta amince ba za ta taɓa mallakar makamin nukiliya ba, “ko ta hanyar saya, kera shi, ko kowace irin hanya ta daban”.

Ya ce da zarar an sanya hannu kan matakin farko, mashigar Hormuz za ta kasance “a buɗe ga kowa".

Shugaban na Amurka ya ƙara da cewa “idan komai ya lafa” Amurka za ta “kwashe ragowar sinadaran Nukiliya” da ke Iran sannan ta “lalata su”.

Abin da Iran ta ce yarjejeniyar ta kunsa

Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana a ranar Juma'a, 12 ga watan Yunin 2026 cewa yarjejeniyar ta ƙunshi abubuwa 14, inda na farko shi ne ɗage takunkumin da Amurka ta sanya wa tashoshin jiragen ruwa na Iran.

Ya ce yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) ta yi kira da a kawo ƙarshen yaki a duk wuraren da ake fada, har da ƙasar Lebanon, da kuma yarjejeniyar rashin tayar da yaƙi ko yin amfani da ƙarfi, tashar Aljazeera ta kawo rahoton hakan.

Kara karanta wannan

Shugaba Trump ya ragargaji Iran duk da shirin kulla yarjejeniya

Iran ta yi bayani kan kulla yarjejeniya da Amurka
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi Hoto: @Araghchi
Source: Twitter

Ministan harkokin wajen ya ƙara da cewa za a saki kuɗaɗen Iran da aka rike da zarar an sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna.

Abbas Araghchi ya ce za a tattauna batun nukiliya a mataki na biyu, kuma matsayar Iran ita ce cewa ya kamata a rage ƙarfin sinadarin uranium da aka inganta a cikin ƙasar.

Ya ƙara da cewa mataki na biyu na tattaunawar zai fi mayar da hankali ne a kan janye takunkuman da Amurka ta sanya wa ƙasar.

'Yan majalisa sun caccaki Shugaba Trump

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan majalisa na jam'iyyar Democrats sun ragargaji Shugaba Donald Trump kan shirin kulla yarjejeniya da Iran.

Sanata mai wakiltar California, Adam Schiff, ya bayyana cewa a baya sun saba jin hakan, amma sai a ji shiru kamar maye ya ci shirwa.

'Dan majalisa Seth Moulton ya bayyana yiwuwar yarjejeniyar a matsayin asalin mika wuya ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng