An Zo Wajen: Israila Ta Shirya Bijirewa Amurka kan Lebanon
- Miistan tsaron Israila, Israel Katz, ya yi maganar janye dakarun sojojin kasarsa daga Kudancin Lebanon da ake yaki da Hezbollah
- Israel Katz ya bayyana cewa dakarun sojojin Israila za su ci gaba da zama a Kudancin Lebanon domin ba mutanen Arewacin kasarsa kariya
- Ministan tsaron na Israila ya nuna cewa idan Amurka ta nemi a janye sojojin daga Kudancin Lebanon, ba za su yi biyayya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tel-Aviv, Israila - Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz, ya nuna cewa sun shirya yi wa Amurka turjiya kan Kudancin Lebanon.
Ministan tsaron na Israila ya bayyana cewa dakarun IDF ba za su janye daga Kudancin Lebanon ba ko da Amurka ta buƙaci hakan.

Source: Twitter
Israila za ta yi turjiya ga Amurka
Jaridar Haaretz ta kawo rahoto a ranar Laraba, 24 ga watan Yunin 2026 cewa Israel Katz, ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron MUNI EXPO 2026.
Israel Katz ya bayyana cewa Isra'ila ba za ta janye dakarunta daga kudancin Lebanon ba "ko da kuwa akwai buƙatar Amurka ta yin hakan."
Lamarin dai zai sanya 'yan gudun hijira 'yan Lebanon mutane 200,000 su koma waɗanda ba za su sake komawa matsugunansu, tashar Aljazeera ta kawo rahoton.
Israila ba za ta bar Lebanon ba
“Ba za a samu fararen hula kuma ba za a sami 'yan ta'adda ba. Me yasa? Saboda abin da ya faru a baya a shiyyoyin tsaro inda akwai fararen hula shi ne, an riƙa samun abubuwan fashewa da hare-hare da ake kai wa sojoji, saboda haka, ba za mu yadda da hakan ba."
"Sojoji suna ciki, mazauna suna waje. An lalata ababen more rayuwa, gidajen suna da haɗari kuma sun rushe. Ba za mu janye ba.”
“Muna da gagarumar nasara da ta fara da mummunar barazana a ranar 7 ga watan Oktoba. Tun daga lokacin, daukacin al'umma, shugabanci, da rundunar soji sun yi aiki da babban ƙuduri."
"Ban san da wani yanayi ba da za a ce, ba tare da wancan mummunar barazana ba, wani zai shiga don magance ramukan ƙarƙashin ƙasa a Gaza.”

Kara karanta wannan
Abin tausayi: Ɗan kasuwa ya mutu a wani yanayi a ɗakin fitacciyar 'yar TikTok a jihar Kano
- Israel Katz

Source: UGC
Israila za ta ci gaba da zama a Syria
Israel Katz ya kuma ƙara da cewa Isra'ila ba za ta janye daga yankunan da ta mamaye a Syria ba ma baki ɗaya.
“Wannan ita ce koyarwar tsaro. Dole ne dakarun IDF su kasance a ɓangaren maƙiyi kuma su kare al'ummomi daga cikin yankin kansa.”
- Israel Katz
Israila ta yi barazanar kai hari Syria
A wani labarin kuma, kun ji cewa Ministan harkokin wajen Isra’ila, Amichai Chikli, ya yi barazanar cewa Isra’ila za ta yaƙi Syria ko ba dade ko ba jima saboda barazana ce a gare ta.
A cewar Ministan, za su yaƙi Syria, ko ba dade ko ba jima, domin ita da Turkiyya sun fi tayar da hankalin Israila fiye da kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Ministan na Isra’ila ya sha yin suka ga ƙasashen yankin da ke taka rawa a ƙoƙarin diflomasiyya na kawo ƙarshen rikice-rikicen da ake fama da su.
Asali: Legit.ng
