Sheikh Baffa Hotoro Ya Shiga Babbar Matsala kan Taba Mutuncin Marigayi Sheikh Dahiru Bauchi
- Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanya 19 ga Oktoba, 2026 domin gurfanar da Sheikh Adam Zubair Adam, wanda aka fi sani da Baffa Hotoro
- Ana tuhumar malamin da zargin bata sunan marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi da Sheikh Munir Adam Koza
- Rahotanni sun nuna cewa an dage shari’ar sau da dama saboda rashin halartar wanda ake tuhuma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Za a gurfanar da malamim addinin Musulunci a Kano, Sheikh Adam Zubair Adam, wanda aka fi sani da Baffa Hotoro a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Kotun ta zabi ranar 19 ga watan Oktoban 2026 domin gurfanar da shi kan zargin bata sunan marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi da Sheikh Munir Adam Koza ta kafafen sadarwa.

Source: Facebook
Rahoton da Aminiya ta wallafa ya nuna cewa Shugaban hukumar ’Yan Sandan Najeriya ne ya shigar da ƙara kan malamin bisa tanadin Dokar Laifukan Intanet ta Najeriya.
Yadda Baffa Hotoro ya ki zuwa kotu
An kama Sheikh Baffa a watan Fabrairu 2026 kafin daga bisani a ba shi beli. An tsara gurfanar da shi a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ranar 23 ga Afrilu 2026, amma bai bayyana a kotu ba.
Daga nan kotun ta sanya ranar 21 ga Mayu domin a gurfanar da shi. Sai dai a wannan ranar ma, bai halarci zaman ba, kuma babu wani lauya da ya bayyana a madadinsa. Saboda haka, kotun ta dage shari’ar zuwa 22 ga Yuli, 2026.
A zaman da aka yi daga baya, wanda ake tuhuma bai sake bayyana a kotu ba. Sai dai lauyansa, Amos, ya gabatar da takardar likita da ke nuna cewa Hotoro na fama da rashin lafiya, don haka ba zai iya halartar zaman ba.

Kara karanta wannan
'Yan sanda sun cafke fasto da sojoji kan shirya sace matan manyan malaman addini a Plateau
Kalaman Baffa Hotoro ya suka tada kura
Zargin da ake yi wa Sheikh Baffa Hotoro ya samo asali ne daga wasu kalamai da ake zargin ya yi kan Sheikh Dahiru Usman Bauchi da Sheikh Munir Adam Koza.
A ranar 18 ga Yuni, 2024, an zargi malamin da yin kalaman batanci da cin mutunci kan malaman biyu, ciki har da wasu kalamai da suka shafi akidarsu da kuma iƙirarin cewa ba su da izinin shiga Masallacin Harami da ke Makka.
A baya, Hotoro ya sha bayyana cewa a shirye yake ya kare kansa a gaban kowace kotu a Najeriya.

Source: Facebook
Hukumar DSS ta taba kama malamin
A watan Mayu, 2023, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta kama shi bayan koke-koken jama’a da kuma na Gwamnatin Jihar Kano kan wasu kalamai da ake zargin ya yi game da Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Daga baya an ga Baffa Hotoro a wani bidiyo yana neman afuwa ga Sheikh Dahiru Bauchi, iyalansa da mabiyansa.

Kara karanta wannan
Bincike ya zo ƙarshe, an ji dalilin Kanal Mohammed Ma'aji na shirya yi wa Tinubu juyin mulki
Sai dai bayan rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi a watan Nuwamba 2025, an sake ganin Hotoro a wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, inda ake zargin ya sake yin kalaman cin mutunci kan marigayin.
Rahotannin sun nuna cewa an dauki kalaman da muhimmanci saboda yiwuwar haifar da rikici tsakanin kungiyoyin addini da kuma barazana ga tsaro.
NHRC ta nemi a kama Sheikh Jingir
Kun ji cewa hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Kasa (NHRC) ta yi magana kan kalaman da Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi.
NHRC ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta kama tare da gurfanar da Sheikh Yahaya Jingir, kan zargin kalaman kiyayya da tunzura jama’a.
Hukumar ta ce ta kalli bidiyon cikin matukar damuwa, inda ta ce malamin ya fito fili yana neman goyon bayan siyasar da ta ware wasu addinai gabanin babban zaben da ke tafe.
Asali: Legit.ng
