NDC: "Yanzu Muka Gano Dalilin Gwamna Abba na Komawa APC"

NDC: "Yanzu Muka Gano Dalilin Gwamna Abba na Komawa APC"

  • Jam’iyyar NDC a jihar Kano ta mayar da martani ga kalaman hadimin gwamna Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature D-Tofa a jab Rabi'u Musa Kwankwaso
  • Jam’iyyar ta kuma nemi gwamnatin Kano ta fito da bayanai game da kuɗin da aka ce ta fitar domin gina wata makaranta, amma aka gano cewa babu ita ko alama
  • Mai magana da yawun jam’iyyar NDC a Kano, Hon. Yusuf Fasaha Majidadi, ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da Legit Hausa a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Jam'iyyar NDC ta mayar wa da hadimin gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Toa martani game da kalamansa na cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na lissafa awakinsa.

Mai magana da yawun jam'iyyar a Kano, Hon. Yusuf Fasaha Majidadi, ya kalubalanci gwamna Abba Akbir Yusuf ya game da Naira miliyan 235.4 aka ware domin gina wata makaranta amma babu aikin, babu dalilinsa.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauke kwandon alheri a jami'o'in jihar 2

NDC ta kalubalanci gwamnatin Abba
Hon Yusuf Fasaha, Gwamna Abba Kabir Yusuf Hoto; Yusuf Fasaha/Hon Salisu Muhammad Kosawa
Source: Facebook

Wani bincike da Track ta wallafa a shafin X ya yi zargin cewa an fitar da kudin da zummar gina ajujuwa da ofisoshi a makarantar sakandaren mata ta Massu a karamar hukumar Sumaila.

A hira da ya yi da Legit, Hon. Fasaha ya bayyana cewa sun samu labarin binciken, kuma suna jira Gwamna ya fito da kansa ya karyata sannan ya nuna wurin da aka yi aiki.

NDC ta kalubalanci gwamnatin Kano

A binciken wanda da ICIR ta wallafa, ta ce binciken ya tabbatar da cewa babu wata makaranta ta GGSSS a yankin Massu na karamar hukumar Sumaila ballantana aikin da aka yi.

A martanin Fasaha, ya ce:

"Abin da yake faruwa a Kano abin takaici ne, abin ƙaico. Ko da yake sai hali ya zo ɗaya, abota ta ke zuwa ɗaya. Yanzu jiha kamar Kano, a ce an fitar da kuɗi na gyaran makarantu, na gyaran ajujuwa, an je an bincika babu."

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana da limaman Katolika suka cire tsoro, sun ja da Tinubu

Ya ƙara da cewa wannan batu ba ’yan adawa ne suka jawo shi ba, magana ce da wata ƙungiya ta bincika, ta kuma gano cewa an fitar da wannan kuɗi, kuma babu aikin.

Hon. Fasaha ya yi zargin cewa ashe Abba Kabir Yusuf ya koma APC ne saboda ya yi mulki irin wanda Bola Ahmed Tinubu ke yi wa Najeriya.

NDC ta kuma waiwayi kalaman Sanusi Bature Dawakin Tofa, da ya bayyana cewa ya hango jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, yana lissafa awakinsa.

NDC ta ce Abba ya koma APC ne saboda hali ya zo daya da Tinubu
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf Hoto: Hon. Salisu Muhammad Kosawa
Source: Facebook

Jam'iyyar ta ce:

"Maganar da Sanusi Bature ke yi cewa mai girma Peter Obi yana da aladu, mai girma Atiku yana da shanunsa, shi kuma Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, jagoran Kwankwasiyya na duniya, yana da awakinsa."
"To muna so mu gaya masa, shi ma mai girma Bola Tinubu yana da jakunansa, kuma a cikin jakunan akwai wanda ya saya, akwai wanda ya haifa da kansa a ƙarƙashin jam’iyyarsa. Saboda haka a jihar Kano muna so mu gaya masa akwai babban auraki, idan lokaci ya yi za mu zo mu kama suna mu gaya masa."

Kara karanta wannan

'Kwankwasiyya ce ta daga Abba': NDC na shirin fattakar gwamnatin Kano a 2027

Mataimakin gwamnan Kano ya jawo rudani

A wani labarin kuma kun ji cewa mataimakin gwamnan Kano, Murtala Sule Garo, ya halarci Mauludin Sheikh Ahmad Tijjani, wanda aka gudanar a fadar Aminu Ado Bayero ta Nasarawa.

An gudanar da taron ne a daidai lokacin da takaddamar masarautar Kano ke ci gaba tsakanin Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II a kan halaccin mulkin masarautar tun bayan da gwamna ya hau mulki.

Masu halartar Mauludin sun nuna damuwa kan rashin amincewa da amfani da filin wasa na Sani Abacha duk da dai an ga kusa a gwamnatin Kano ya halarci zaman, wanda hakan kuma ya jawo maganganu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng