An Dage Ci Gaba da Tattaunawar Amurka da Iran duk da Sanya Hannu kan Yarjejeniya

An Dage Ci Gaba da Tattaunawar Amurka da Iran duk da Sanya Hannu kan Yarjejeniya

  • Kasashen Amurka da Jamhuriyar Iran sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna domin kawo karshen yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya
  • Bayan rattaba hannun, an shirya za a gudanar da tattaunawa domin ci gaba da bin sawun yarjejeniyar a kasar Switzerland tsakanin kasashen da lamarin ya shafa
  • A ranar da aka shirya za a fara tattaunawar, sai kasar Switzerland ta fito ta bayyana cewa an dage ta, inda ta bar mutane cikin duhu kan sabon lokacin da za a yi ta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Kasar Switzerland - Switzerland ta sanar da cewa an dage shirin tattaunawar da aka tsara yi domin ci gaba da bin sawun yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin Gabas Ta Tsakiya.

Sanarwar na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan soke tafiyar Mataimakin shugaban Amurka JD Vance zuwa ƙasar Switzerland.

Kara karanta wannan

Hashim: Dan takarar shugaban kasa a Najeriya ya yi magana kan yarjejeniyar Amurka, Iran

An dage tattaunawa tsakanin Amurka da Iran a Switzerland
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian da Shugaba Donald Trump na Amurka Hoto: @depezeshkian, @realDonaldTrump
Source: Twitter

Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa ma'aikatar harkokin wajen Switzerland ce ta sanar da hakan, cikin wata sanarwa a ranar Juma'a, 19 ga watan Yunin 2026.

Iran, Amurka sun sanya hannu a yarjejeniya

Sanya hannu a kan yarjejeniyar a wannan makon an yi shi ne da nufin kawo ƙarshen rikici a Iran, sake buɗe mashigar Hormuz, da kuma fara wa'adin kwanaki 60 na tattaunawa kan batutuwa masu faɗi, tare da shirin nukiliyar Tehran.

A lokaci guda, yarjejeniyar ta kasance domin dakatar da faɗace-faɗace a ƙasar Lebanon, amma rundunar sojojin Isra'ila ta sanar da cewa ta kai sababbin hare-hare a kan sansanonin Hezbollah da ke kudancin ƙasar.

An dage tattaunawar da aka shirya

Ma'aikatar harkokin wajen Switzerland ta sanar da cewa ba za a gudanar da tattaunawar ba, kamar yadda aka tsara tun da farko.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

“An dage shirin tattaunawar da aka tsara gudanarwa tsakanin Amurka, Iran, Qatar, da Pakistan."

Kara karanta wannan

"Yan hassada ne": Trump ya hasala kan masu sukar yarjejeniyar Amurka da Iran

“Switzerland tana nan a shirye domin zama mai shirya wannan tattaunawa. Ana ci gaba da ayyukan shirye-shirye da suka dace a Burgenstock."

Sanarwar dai ta kare ne ba tare da bayar da sabuwar rana ta gudanar da tattaunawar ba tsakanin kasashen da abin ya shafa.

An dage tattaunawar Amurka da Iran
Shugaba Donald Trump a wajen yakin neman zabe Hoto: Donald J Trump
Source: Facebook

JD Vance ya fasa zuwa Switzerland

Wannan yana zuwa ne bayan sanarwar da fadar White House ta fitar a ƙarshen ranar Alhamis, 18 ga watan Yunin 2026 cewa an soke tafiyar JD Vance.

A ƙasar Iran, kamfanin dillacin labarai na Tasnim ya bayyana cewa “babu abun da aka tabbatar” game da tafiyar tawagar Iran zuwa ƙasar Switzerland, tashar Reuters ta kawo rahoton.

Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Iran Masoud Pezeshkian sun sanya hannu a kan yarjejeniyar daban-daban.

Shugaban Iran ya yaba wa yarjejeniyar sulhu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi martani kan yarjejeniyar da kasarsa ta cimmawa da Amurka domin kawo karshen yaki.

Masoud Pezeshkian ya yaba da sabuwar yarjejeniyar fahimtar juna da aka kulla tsakanin Iran da Amurka wanda ya kawo karshen yaƙi a Gabas ta Tsakiya.

Shugaba Pezeshkian ya ce takardar da ke kunshe da yarjejeniyar ta nuna muryar al’umma daya da ba ta sayar da daraja da ‘yancinta ga kowace barazana ko matsin lamba ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng