Sowore: An Samu Dan Takarar da Zai Dawo da Tallafin Fetur idan Ya Ci Zabe

Sowore: An Samu Dan Takarar da Zai Dawo da Tallafin Fetur idan Ya Ci Zabe

  • Ɗan takarar AAC na 2027, Omoyele Sowore, ya ce ya yi magana kan maido da tallafin fetur idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasar Najeriya
  • Sowore ya ce gwamnati na ci gaba da biyan wasu nau’ikan tallafi duk da cewa ta cire tallafin fetur
  • Ɗan siyasar ya ce masu hannu da shuni ne suka fi cin gajiyar tallafin gwamnati ta hanyar rangwamen haraji da kwastam

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na African Action Congress (AAC) a zaɓen 2027, Omoyele Sowore, ya bayyana matsayarsa kan dawo da tallafin man fetur.

Omoyele Sowere ya ce zai maido da tallafin fetur idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban kasar Najeriya.

Omoyele ya ce zai dawo da tallafin fetur
Omoyele Sowore dan takarar shugaban kasa na AAC Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

Sowore ya bayyana hakan ne a wata hira da Arise tv ranar Talata, 11 ga watan Agustan 2026 yayin da yake bayyana wata hanya ta daban da yake ganin za a bi wajen magance matsalolin tattalin arzikin Najeriya.

Kara karanta wannan

Fitaccen mawaki ya ɗauki abubuwan da ke faruwa a Najeriya ya kai gaban shugaban Amurka

Sowore zai maido da tallafi

Da aka tambaye shi ko zai dawo da tallafin fetur idan ya zama shugaban ƙasa, Sowore ya amsa da cewa: “Tabbas.”

Ya ce gwamnatin tarayya har yanzu tana biyan wasu nau’ikan tallafi a tattalin arzikin ƙasar duk da cewa ta cire tallafin man fetur.

“Da farko dai, har yanzu suna biyan tallafi. Sun sauya sunan abin da suke kiran shi ne kawai. Ba fetur kaɗai suke tallafawa ba, saboda ba su da isasshen fetur kuma ba za su iya samar da shi a cikin gida ba, suna kuma tallafa wa Naira. Wannan shi ne abin da ba za su taɓa gaya muku ba,” in ji shi.

Sowore ya kuma ce ana tallafa wa darajar Naira ta hanyar wasu tallafi da ake gudanarwa cikin “shiru da ɓoye”.

“Dalilin da ya sa Naira take da wani ƙayyadadden farashi idan aka kwatanta da dala shi ne saboda ana tallafa mata a hankali kuma a ɓoye,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Zaben Osun: Saura kwana 5 a fara kada kuri'a, an bankado makarkashiyar da ake kullawa

Ya yi magana kan tallafin Naira

Da yake mayar da martani kan hujjar cewa ƙasashe kan tallafa wa kuɗaɗensu, Sowore ya ce matsalar ita ce rashin gaskiya da bayyana gaskiyar abin da gwamnati ke yi wajen tallafin.

“Eh, amma me ya sa kuke ƙarya game da tallafi? Kun sani, dole ne mu daina faɗin ƙarya game da... Abin da kowa ya amince da shi shi ne, ba wai tallafi mummunan abu ba ne, domin babu ƙasar da ke duniya da ba ta tallafa wa talakawanta,” in ji shi.

Ya ce masu hannu da shuni a Najeriya ne suka fi cin gajiyar tallafin gwamnati fiye da talakawa, inda ya kawo misalin rangwamen da ake bai wa masu shigo da kaya ta hukumar kwastam.

Sowore zai dawo da tallafin man fetur
Da takarar shugaban kasa na AAC, Omoyele Sowore Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

Kotu ta bayar da belin Sowore

A wani labarin kuma, kun ji cewa mai shari'a Mohammed Umar na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya amince da bayar da belin Naira miliyan 200 ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore.

Omoyele Sowore dai yana fuskantar shari'a ne a gaban kotun kan cin mutuncin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng