Abin da Ya Kora Tsohon Shugaban DSS Mai Neman Takarar Gwamna daga ADC

Abin da Ya Kora Tsohon Shugaban DSS Mai Neman Takarar Gwamna daga ADC

  • Lawal Musa Daura bai dade a jam’iyyar ADC ba sai aka ji ya sauya sheka saboda zargin rashin yin adalci
  • Tsohon shugaban na DSS ya koma APM makonni bayan rasa takarar gwamnan jihar Katsina a zaben badi
  • Alhaji Daura ya dage sai ya canza akalar siyasar Najeriya daga karya da yaudara da ake yi wa jama’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Katsina - Lawal Musa Daura wanda ya rike shugabancin hukumar DSS ya sauya sheka daga jam’iyyar ADC mai hamayya.

Lawal Musa Daura da wasu magoya bayansa sun rabu da tafiyar ADC, suka shiga jam’iyyar adawar nan ta APM mai alamar rogo.

Lawal Musa Daura mni
Tsohon mai neman takarar gwamnan Katsina a ADC, Lawal Daura Hoto: Lawal Musa Daura mni
Source: Facebook

Lawal Daura ya ga rashin adalci a ADC

Rahoton jaridar Daily Trust ya ce Alhaji Lawal Musa Daura ya fake da zargin rashin adalci a jam’iyyar ADC wajen sauya-sheka.

Kara karanta wannan

Magana ta ƙare, Jami'ar Kano ta faɗi gaskiya kan zargin Sarki Sanusi II ya faɗi jarabawa

Tsohon jami’in tsaron ya yi watsi da zargin da ake yi cewa ya rabu da ADC ne saboda bai samu takarar gwamnan jihar Katsina ba.

Lawal Daura ya ce dama tun tuni ya yi sallama da jam’iyyar kuma ya yi tsit ne saboda ya iya yin nazarin mataki na gaba da zai dauka.

Da farko ya ce sun yi kuskuren shiga jam’iyyar ADC wanda ya bayyana ta da kyakkyawar mota amma maras inji mai isasshen lafiya.

A lokacin da ya ayyana niyyar yin takara tun kafin ya yi rajista da ADC, ya ce tamkar matafiyi ne da ya isa tasha yana neman motar shiga.

A tattaunawar da DCL Hausa ta yi da shi da Legit Hausa ta saurara, an ji yana cewa ba don komai ya fada siyasa ba illa domin taimakon jama’a.

Ya ce:

“Na rike mukamin da ya fi na gwamna, iko da mulki da kudi da komai.”

Kara karanta wannan

Ahmad Gumi ya waiwayi Sheikh Jingir saboda maganar tallar tikitin Muslim Muslim

Sauya-shekar Daura daga ADC zuwa APM

Ko da a ce ya samu takarar gwamna a jam’iyyar ADC, ya ce da sai ya canza-sheka a yanzu.

Da yanzu ya koma APM, ya bayyana jam’iyyar a matsayin wanda ta fi lafiya, kuma yana ganin cewa ita ce mafita a zabe mai zuwa.

Burin Lawal Daura mai neman zama gwamna a zaben 2023 shi ne ya gyara siyasa, ra’ayin mutane ya canza daga yadda yake a yau.

Da aka tambaye shi ko samun takarar mataimakin shugaban kasa a APM ta sa ya sauya-sheka, sai ya ce ‘yan jarida su dakata tukuna.

Nan da mako mai zuwa Alhaji Daura ya ce duniya za ta san makomarsa a jam’iyyar APM.

Lawal Daura da Mustapha Inuwa sun bar ADC

Rahoto ya gabata cewa manyan jiga-jigan siyasa biyu a jihar Katsina, Dr. Mustapha Muhammad Inuwa da Lawal Musa Daura, sun yi murabus daga ADC.

Dr. Mustapha Inuwa ya raba gari da jam'iyyar zuwa APC bayan ya ƙi amincewa da nasarar Sanata Ahmad Babba Kaita a matsayin ɗan takarar gwamna.

Shi kuma tsohon Darakta-Janar na DSS, Lawal Musa Daura, ya koma jam'iyyar APM inda ake hasashen zai samu babban takara a zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng