Majalisa Ta Juya wa Trump baya, Ta Bada Umarni a Janye Sojojin Amurka daga Iran
- Majalisar Amurka ta amince da wani kudiri da ke neman takaita ikon Shugaba Donald Trump kan ci gaba da amfani da sojojin Amurka a rikicin Iran
- Kudirin ya samu goyon bayan ‘yan Republican da yawancin ‘yan Democrat, lamarin da ya zama babban kalubale ga gwamnatin Trump
- Duk da wannan ci gaba, ana ganin kudirin ba zai yi tasiri ba saboda gwamnatin Trump na cewa sojojin Amurka ba sa cikin yaki kai tsaye da Iran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - A ranar Talata, majalisar dattawan Amurka ta amince da wani kudiri da majalisar wakilai ta gabatar wanda ke neman takaita ikon Shugaba Donald Trump kan yadda ake tafiyar da rikicin Iran.
Wannan ne karon farko da irin wannan kudiri ya samu nasarar wucewa a majalisun dokokin Amurka biyu, abin da ke nuna wani sabon kalubale ga shugaban kasar kan yadda yake gudanar da rikicin.

Source: Getty Images
Majalisa ta amince a takaita ikon Trump
A kuri’u 50 bisa 48, ‘yan Republican hudu — Susan Collins daga Maine, Bill Cassidy daga Louisiana, Lisa Murkowski daga Alaska da Rand Paul daga Kentucky — sun goyi bayan kudirin tare da mafi yawan ‘yan Democrat, in ji rahoton CBS News.
Sai dai Sanata John Fetterman daga Pennsylvania, wanda yake cikin ‘yan Democrat, ya kada kuri’ar adawa da kudirin. Sanatocin Republican biyu, Mitch McConnell da Dave McCormick, ba su halarci kada kuri’ar ba.
Kudirin ya bukaci Shugaba Trump ya janye dakarun Amurka daga duk wani yaki ko rikici da Iran, sai dai idan majalisa ta ayyana yaki ko ta bayar da cikakken izinin amfani da karfin soji.
Matakin ya dogara ne kan dokar ikon yaki ta shekarar 1973 wadda ta bai wa majalisa damar bukatar shugaban kasa ya janye sojoji daga rikici idan ba a samu amincewar majalisar ba.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Trump ya sake barazanar kai hari mai zafi a Iran duk da fara tattaunawa
Saboda kudirin bai bukatar sa hannun shugaban kasa, zai iya zama doka ba tare da amincewar Trump ba.
Gwamnatin Trump ta yi watsi da tasirin kudirin
Sai dai ana ganin kudirin ba zai yi tasiri sosai ba saboda gwamnatin Trump na cewa sojojin Amurka ba sa cikin wani yaki kai tsaye da Iran a halin yanzu.
The Washington Post ta rahoto wasu jami’an gwamnatin sun kuma bayyana cewa suna ganin dokar ikon yaki ta 1973 ba ta dace da tsarin mulkin kasar ba.
Dan Majalisar Wakilai Gregory Meeks daga New York, wanda ya gabatar da kudirin, ya ce zai binciki duk hanyoyin doka domin ganin bangaren zartarwa ya mutunta bukatar majalisa.
Ya ce majalisa ba ta taba amincewa da yakin da ake yi ba, kuma shugaban kasa ba shi da ikon ci gaba da tafiyar da irin wannan lamari na tsawon lokaci ba tare da amincewar Majalisa ba.

Source: Getty Images
'Yan Democrat sun matsa wa Republican lamba
Shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Chuck Schumer, ya bukaci ‘yan Republican su goyi bayan kudirin, yana mai cewa ya kamata su bayyana matsayinsu kan rikicin.
Schumer ya ce ‘yan Republican na iya sukar yadda ake gudanar da yakin a boye, amma hanya daya tilo da za a kawo karshen rikicin ita ce su dauki mataki a majalisa.
Matakin na majalisar dattawa ya zo ne a daidai lokacin da wasu ‘yan Republican ke kara nuna damuwa kan yadda ake tafiyar da rikicin Iran.
Tun bayan fara yakin a karshen watan Fabrairu, ‘yan Democrat sun tilasta kada kuri’a kan batun ikon yaki sau goma a Majalisar Dattawa domin matsa lamba kan gwamnatin Trump.
Amurka ta sassauta wa 'yan wasan Iran
A wani labari, mun ruwaito cewa, yayin da ake ci gaba da gasar cin kofin duniya a Amurka, kasar ta sassauta takunkumi kan tawagar kwallon kafa ta Iran.
Sabuwar dokar ta bai wa tawagar Iran damar shiga Amurka kwanaki biyu kafin wasansu na gaba maimakon kwana daya kadai.
Iran ta nuna rashin jin dadi kan takunkumin, tana mai cewa hakan ya jefa tawagar cikin wahala yayin zirga-zirga tsakanin Mexico da Amurka.
Asali: Legit.ng

