Magana Ta Kare, Jami'ar Kano Ta Fadi Gaskiya kan Zargin Sarki Sanusi II Ya Faɗi Jarabawa
- Jami’ar Northwest ta jihar Kano ta musanta wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta kan karatun Sarki na 16, Muhammadu Sanusi II
- Jami’ar ta ce zargin cewa Sarki Sanusi ya fadi jarabawa a wasu darussa da yake karanta ƙarya ne kuma ba shi da tushe
- Ta yi barazanar daukar mataki kan duk wanda ya kirkiri ko ya yada bayanan da suka shafi zargin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Jami’ar Northwest ta Kano (NWUK) ta musanta wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, wanda ke dauke da ikirarin cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya faɗi wasu darussa.
Jami’ar ta bayyana bidiyon da rubuce-rubucen da aka danganta da shi a matsayin ƙarya, marasa tushe kuma na yaudara, tana mai cewa babu wata hujja da ke tabbatar da zargin da ake yadawa.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa jami’ar NWUK ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na jami’ar, Abubakar Ibrahim, ya fitar ranar Talata a Kano.
Jami’ar NWUK ta musanta bidiyon
A cewar sanarwar, bidiyon da ake magana a kai ya nuna Sarki Sanusi ne yayin da yake halartar wata lacca ta jama’a da kungiyar International Humanitarian Law Society ta shirya a jami’ar.
Sai dai bayan bidiyon ya yadu, wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun hada shi da rubuce-rubucen da ke zargin cewa Sarkin ya taba samun carry-over a lokacin karatunsa.
Sanarwar ta ce wasu daga cikin masu yada bayanan sun kai wa jami’ar tambaya domin neman karin bayani kan abin da suka kira gazawar karatun Sarkin.
Ta ce zargin ba shi da tushe
Sai dai hukumar jami’ar ta yi watsi da zargin, tana mai cewa bidiyon da rubuce-rubucen da aka danganta da shi ba su fito daga gare ta ba.

Kara karanta wannan
Jami'ar ABU ta waiwayi Farfesa Abdullahi, wanda aka ce yana da PhD 5, MSc 5 da digiri 7
A cikin sanarwar, jami’ar ta ce:
“Zargin gaba daya ƙarya ne, ba shi da tushe, duk yaudara ce kuma babu ko hujja ko daya da ke tabbatar da shi.”
NWUK ta kuma bukaci daukacin al’ummar jami’ar da sauran jama’a da su yi watsi da bidiyon, rubuce-rubucen da kuma duk wasu ikirarin da suka samo asali daga bayanan.
NWUK ta yi barazanar daukar mataki
Hukumar jami’ar ta kuma yi gargadi kan kirkira, wallafawa ko yada bayanan da ta bayyana a matsayin na ƙarya da kuma bata suna, kamar yadda Daily Post ta kawo.
Ta ce duk wanda aka samu yana da hannu wajen kirkirar ko yada bidiyon ko kuma irin wadannan zarge-zarge za a kai rahotonsa ga hukumomin da abin ya shafa domin daukar matakin da ya dace bisa dokokin Najeriya.

Source: Twitter
Jami’ar ta ce ba za ta amince a yi amfani da sunanta wajen yada bayanan da ba su da inganci ba, musamman wadanda za su iya bata sunan jami’ar ko wasu mutane.
NWUK ta shawarci jama’a da su rika dogaro da sanarwar hukuma daga jami’ar idan suna bukatar samun sahihin bayani kan ayyukanta da al’amuran da suka shafi makarantar.
Sarkin Kano ya ja hankalin shugabanni
A baya, kun ji cewa Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa duk wata manufar tattalin arziki da ba ta inganta walwalar al'umma ba, ba za a iya cewa ta yi nasara ba.
Ya bukaci shugabanni su mayar da hankali kan rage talauci, inganta rayuwa da samar da ci gaban da kowa zai amfana da shi.
Asali: Legit.ng

