Isra’ila Ta Ci Gyaran Iran a Yarjejeniya da Amurka game da Dakarunta a Lebanon
- Ministan Tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya yi magana game da yarjejeniyar Amurka da Iran a yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya
- Katz ya bayyana cewa Isra’ila ta sanar da matsayinta karara cewa ba za ta janye dakarunta ba, yana mai kiran hakan nasarar diflomasiyya.
- Ya ce shugabannin Isra’ila sun fadawa jami’an Amurka cewa kasancewar sojoji a yankin na da muhimmanci wajen kare mazauna arewacin kasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tel Aviv, Israel - Ministan Tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya yi karin haske game da yarjejeniyar kasar Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Katz ya bayyana cewa Amurka ba ta nemi Isra’ila ta janye sojojinta daga kudancin Lebanon ba a cikin yarjejeniyar.

Source: Getty Images
Ya yi wannan bayani ne ranar Laraba 24 ga watan Yunin 2026 yayin wata ganawa da shugabannin kananan hukumomi da aka gudanar a birnin Tel Aviv, cewar Al Jazeera.
Matsayar Isra'ila game da yarjejeniya da Iran
Rahotanni sun nuna cewa batun janye sojojin Isra’ila ya kasance daya daga cikin sharuddan da Tehran ta gabatar domin tsagaita wuta a yakin da ake yi.
Sai dai Katz ya ce Isra’ila ta riga ta bayyana cewa ba za ta janye dakarunta daga yankin ba a kowane hali.
Ya kara da cewa har zuwa yanzu babu wata bukata daga gwamnatin Amurka da ke neman a janye sojojin.
A cewarsa, rashin samun irin wannan bukata daga Amurka wata babbar nasara ce ta bangaren diflomasiyya ga Isra’ila.
Lokacin da aka tambaye shi ko sojojin Isra’ila za su bi umarnin Amurka idan an nemi janyewar, ya bayyana matsayinsu.

Source: Facebook
Abin da Katz ya fada wa takwaransa na Amurka
Katz ya ce ya fada wa Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, dalilin ci gaba da kasancewar sojojin a yankin wanda ke fama da matsalolin tsaro.
Ya kuma ce Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana irin wannan matsayi ga Shugaban Amurka a baya domin tabbatar masa da matsayarsa.
A cewarsa, Netanyahu ya sanar da Donald Trump cewa dakarun Isra’ila na yankin ne domin kare mazauna Arewacin kasar, cewar Times of Israel.
Katz ya jaddada cewa manufar ci gaba da zama a kudancin Lebanon ita ce tabbatar da tsaron al’ummomin da ke kusa da iyaka.
Ya ce gwamnatin Isra’ila na ganin wannan mataki a matsayin muhimmin bangare na kare rayuka da dukiyoyin jama’arta yayin da ae ci gaba da yaki a yankin Gabas ta Tsakiya.
Iran: Yadda Isra'ila ta so taimaka wa masu zanga-zanga
A wani labarin, an ji cewa tsohon Firaministan Isra’ila, Naftali Bennett, ya bayyana cewa kasar ta shigar da na’urorin Starlink a boye zuwa Iran.
Bennett ya bayyana cewa an shirya samar da dubban na’urori domin tabbatar da ci gaba da intanet da kafafen sada zumunta a Iran.
Tsohon Firayim Ministan ya zargi gwamnatin Benjamin Netanyahu da dakatar da shirin, lamarin da ya hana masu zanga-zanga cin gajiyar tsarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

