'Ni ba Kanwar Lasa ba ne': Gwamna Ya Ce Bai Tsoron Tinubu, Gwamnonin APC
- Ana shirin zaben gwamnan Osun, Gwamna Ademola Adeleke, ya bayyana damuwa game da zaben da ake tunkara
- Adeleke ya ce ba ya tsoron karfin gwamnatin tarayya ko goyon bayan wasu gwamnoni ga dan takarar APC a zaben jihar
- Ya bayyana kansa a matsayin “bulldozer”, yana mai cewa gwamnoni abokansa ne, kuma kasancewarsu a Osun ba zai tabbatar da samun kuri’u ga APC ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Osogbo, Osun - Gwamnan Osun kuma dan takarar jam’iyyar Accord, Ademola Adeleke, ya yi magana kan zaben da za a yi.
Adeleke ya ce kwata-kwata ba ya tsoron zargin goyon bayan gwamnatin tarayya da wasu gwamnoni ga APC.

Source: Twitter
Adeleke ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin taron Arise Townhall Meeting, inda ya ce a shirye yake ya tunkari abin da ya kira “karfin gwamnatin tarayya”.
'Ban tsoron gwamnatin tarayya': Gwamna Adeleke
Ya bayyana kansa a matsayin “bulldozer”, yana mai cewa ba ya tsoron karfin gwamnatin tarayya ko goyon bayan gwamnoni ga dan takarar APC.
Ya ce:
"Ni ba kanwar lasa ba ne, ba na tsoron karfin ikon gwamnatin tarayya da goyon bayan gwamnoni ga dan takararsu, idan sun ga dama su kawo suka gwamnonin nan."
Adeleke ya yi watsi da ra’ayin cewa kasancewar gwamnoni masu ci da goyon bayansu ga dan takarar APC na iya sauya sakamakon zaben.
Ya ce gwamnoni da ke goyon bayan dan takarar APC abokansa ne, yana mai jaddada cewa zuwansu Osun ba yana nufin za su samu kuri’u ga abokin hamayyarsa ba.
A cewarsa, gwamnoni suna da damar yin kamfe da tattara goyon baya ga dan takarar APC, amma ba za su iya kada kuri’a a zaben ba, cewar Punch.
"Wadannan gwamnonin abokaina ne, na kware kan tsarin shugabanci, ba zabe za su yi ba, kawai za su zo ne su yi rawa, bayan zaben za mu hadu."

Kara karanta wannan
Dan takarar gwamna ya watsar da jam'iyyarsa, ya marawa APC baya a zaben jihar Osun
- Ademola Adeleke

Source: Original
Adeleke ya musanta kuntatawa a Osun
Haka kuma, Adeleke ya musanta zargin cewa gwamnatinsa ta mayar da Osun sansanin sojoji, yana mai cewa ba shi da ikon tsarin mulki na tura rundunar soji.
Jwaban gwamnan sun zo ne yayin da harkokin siyasa ke kara zafi a Osun, inda jam’iyyun siyasa ke kara kamfe da hada magoya baya gabanin zaben gwamna ranar Asabar.
Zaben ya jawo hankalin jama’a sosai yayin da manyan jam’iyyu da ‘yan takararsu ke kara kokarin samun goyon bayan masu kada kuri’a a sassan jihar.
Adeleke, wanda ke neman sake lashe wa’adi, zai kara da dan takarar APC a zaben da ake sa ran zai kasance mai matukar zafi.
Bangarorin biyu na ci gaba da karfafa sansanoninsu da neman goyon bayan masu kada kuri’a yayin da ranar zaben 15 ga Agusta ke kara karatowa.
Yadda gwamnan Osun ke haɗa rawa da aiki
Mun ba ku labarin cewa Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya ce sha'awar rawa da yake da ita ba ta hana shi sauke nauyin da ke kansa a matsayin gwamna ba.
Adeleke ya ce rawa wani bangare ne na halayensa da kuma abin sha'awa, yana mai cewa ya gudanar da ayyukan raya jihar a fannoni daban-daban.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wani taron masu neman takarar gwamnan Osun da aka shirya gabanin zaɓen ranar 15 ga Agusta.
Asali: Legit.ng

