Rigima Sabuwa: Iran Ta Sake Rufe Mashigar Hormuz, Ta Zargi Trump da Karya Sharadi

Rigima Sabuwa: Iran Ta Sake Rufe Mashigar Hormuz, Ta Zargi Trump da Karya Sharadi

  • Iran ta sake rufe mashigar ruwan Hormuz bisa zargin ci gaba da kasancewar sojojin Amurka da rashin janye sojojin Isra’ila daga Lebanon
  • Rundunar juyin juya hali na IRGC ta ce yarjejeniyar Amurka da Iran ba ta cika ba har sai an bi wasu sharuddan da Tehran ta gindaya
  • Sai dai, wasu rahotanni sun ce zirga-zirgar jiragen ruwa a Hormuz ta dawo karkashin sa ido na Iran bayan rudani kan batun rufe hanyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Iran - Kasar Iran ta sake sanar da rufe mashigar Hormuz, bisa zargin cewa Amurka na ci gaba da ajiye dakarunta a yankin yayin da Isra’ila ba ta janye sojojinta daga kudancin Lebanon ba.

Rahotanni sun ce Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ce ta fitar da umarnin rufe hanyar, tana mai cewa hakan ya samo asali ne daga abin da ta bayyana a matsayin rashin cika sharuddan yarjejeniyar fahimtar juna da Washington.

Kara karanta wannan

"Yan hassada ne": Trump ya hasala kan masu sukar yarjejeniyar Amurka da Iran

Iran ta sake rufe mashigar Hormuz bayan yarjejeniya da Amurka
Wani na nuna mashigar Hormuz da ke kusa da gabar tekun Iran a jikin taswira. Hoto: JULIEN DE ROSA / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

IRGC ta zargi Amurka da karya yarjejeniya

Yarjejeniyar ta kasance wadda Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Iran Masoud Pezeshkian suka rattaba hannu a ranar Laraba, 17 ga Yunin 2026, in ji rahoton The New York Times.

A cikin sanarwar da aka yada ta tashoshin sadarwar ruwa, IRGC ta ce janye dakarun Amurka daga yankin Tekun Fasha da kuma janye sojojin Isra’ila daga Lebanon na daga cikin muhimman sharuddan yarjejeniyar.

Sanarwar ta ce:

“Tun da janye Isra’ila daga Lebanon, kawo karshen takunkumin ruwa gaba daya da kuma janye sojojin Amurka daga yankin na daga cikin manyan sharuddan yarjejeniyar, mashigin Hormuz zai kasance a rufe har sai an cika wadannan sharudda.”

Kungiyar ta kuma gargadi jiragen ruwa da su nisanci mashigar, tana mai cewa duk wani jirgin da ya karya umarnin zai fuskanci mataki.

Amurka ta ce ta dage takunkumi

Rundunar Tsaron Amurka ta CENTCOM ta bayyana cewa ta cire matakin hana zirga-zirgar jiragen ruwa zuwa tashoshin Iran da ta shafe watanni biyu tana aiwatarwa.

Kara karanta wannan

Isra'ila za ta shiga uku, Iran ya yi mata gagarumar barazana game da Lebanon

Sai dai ba a bayyana dalilin da ya sa Iran ta ce ba a kammala cire takunkumin gaba daya ba ba, in ji rahoton The Cable.

Wannan sabanin ra’ayi ya kara nuna bambancin fahimta tsakanin bangarorin biyu kan yadda ake aiwatar da yarjejeniyar.

Rahotanni sun ce an dawo da zirga zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz
Yadda jirage ke zirga-zirga a mashigar ruwa ta Hormuz a Iran Hoto: Anadolo via Getty Images
Source: Getty Images

Zirga-zirga ta dawo a Hormuz

Sai dai, wani sabo rahoto na nuni da cewa an dawo da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin Hormuz bayan sanarwar rufe shi da aka watsa ta rediyon jiragen ruwa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei, ya ce dakarun kasar sun dauki matakan da suka dace domin tabbatar da zirga-zirgar jiragen kasuwanci cikin tsaro a mashigar.

A cewar rahotanni, Baghaei ya ce an ci gaba da zirga-zirgar jiragen ruwa a wannan hanya tun bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MOU) da aka cimma domin kawo karshen yakin.

Majalisa ta nemi a janye sojojin Amurka

A wani labari, mun ruwaito cewa, Donald Trump ya soki wata ƙuri'ar da aka kaɗa a Majalisar wakilan Amurka da ke neman ba da umarnin janye dakarun sojojin kasar daga yaƙin Iran.

Kara karanta wannan

Sulhu tsakanin Iran da Amurka ya fusata Isra'ilawa, sun dura kan Netanyahu

Trump ya bayyana kada kuri'ar a matsayin wani mataki na “rashin kishin ƙasa” wanda ya kawo cikas ga tattaunawar da ake yi da birnin Tehran.

A cikin wani babban kalubale ga Trump, mambobi huɗu na jam'iyyarsa ta Republican mai rinjaye sun haɗa gwiwa da 'yan jam'iyyar Democrat wajen marawa matakin baya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com