Tayin da Amurka Ta Yi Wa Iran bayan Fara Tattaunawa a Switzerland

Tayin da Amurka Ta Yi Wa Iran bayan Fara Tattaunawa a Switzerland

  • An fara tattaunawa tsakanin kasashen Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna
  • Wakilan kasashen biyu sun fara tattaunawar ne a kasar Switzerland a ranar Lahadi, 21 ga watan Yunin 2026
  • A yayin tattaunawar, Amurka ta gabatar da bukatarta ga Iran kan shirin nukiliyarta wanda aka dade ana takaddama a kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kasar Switzerland - Amurka da Iran sun fara tattaunawa a kasar Switzerland domin samun fahimtar juna a tsakaninsu.

A yayin zaman tattaunawar na farko, wakilan Amurka sun mika bukata ga Iran kan shirin da take da shi na nukiliya.

Amurka ta yi ga Iran
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian da takwaransa na Amurka, Donald Trump Hoto: @Drpezeshkian, @realDonaldTrump
Source: Twitter

Wane tayi Amurka ta yi wa kasar Iran?

Rahoton tashar Axios ya nuna cewa Amurka ta bukaci Iran ta amince da bai wa masu binciken majalisar dinkin duniya damar duba cibiyoyin nukiliyarta.

Kara karanta wannan

An dage ci gaba da tattaunawar Iran da Amurka.duk da sanya hannu kan yarjejeniya

Wakilan na Amurka sun bayyana cewa a madadin hakan, za a ba Iran damar amfani da wani ɓangare na kudaden da aka ƙwace mata, ciki har da dala biliyan 6 da ke kasar Qatar.

Wasu majiyoyi guda biyu na yankin, sun bayyana cewa Amurka na son a kammala zagayen farko na tattaunawa da wannan yarjejeniya wato Iran ta gayyaci masu bincike zuwa wuraren nukiliyarta.

Amurka na son duba cibiyoyin nukiliyar Iran

Waɗannan cibiyoyi sun taɓa zama wuraren da Amurka da Isra’ila suka kai hare-hare a baya, kuma ba a sake yin bincike cikinsu ba tun watan Yunin shekarae 2025.

Idan Iran ta amince da wannan tayin da aka yi mata, Amurka na shirin ba ta damar samun wasu daga cikin kudadenta da aka ƙwace a ƙasashen waje, inda za a fara da asusun dala biliyan 6 da ke kasar Qatar.

An bayyana cewa ce za a takaita amfani da kuɗin ne ga sayen kayayyakin jin-ƙai kamar abinci da magunguna, ba tare da amfani da shi a wasu harkoki na daban ba.

Amurka ta yi ga kasar Iran kan shirin nukiliya
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Amurka da Iran sun tattauna a Switzerland

An gudanar da tattaunawar duk da iƙirarin da Iran ta yi a ranar Asabar na cewa ta rufe ashigar Hormuz a matsayin martani ga take yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila ta yi a Lebanon.

Kara karanta wannan

"Yan hassada ne": Trump ya hasala kan masu sukar yarjejeniyar Amurka da Iran

Mataimakin shugaban kasar Amurka, JD Vance, ya bayyana a ranar Lahadi, 21 ga watan Yunin 2026 cewa an samu ci gaba a tattaunawar.

“Mun riga mun sami ci gaba a cikin 'yan sa'o'in da suka gabata, kuma ina sa ran za mu samu ƙarin ci gaba a sa'o'i masu zuwa."

- JD Vance

Sanata a Amurka ya soki Trump

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban sanatan jam'iyyar Democratic ta Amurka, Chuck Schumer, ya soki ‘rashin kwarewar’ Shugaba Donald Trump.

Chuck Schumer wanda shi ne shugaban marasa rinjaye na jam'iyyar Democratic a Majalisar dattawan, ya ce Shugaba Trump ya jefa Amurka cikin wani yanayi mafi muni.

Shugaban marasa rinjayen ya bayyana cewa rashin kwarewar Trump da girman kansa sun sanya Amurka cikin matsala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com