Iran Ta Fara Samun Tagomashi daga Turai bayan Tsayar da Yaki da Amurka
- Iran ta fara samun tagomashi bayan ta cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka da za ta kawo ƙarshen yaƙin da ya ɗauki sama da wata uku
- Rahotanni sun nuna cewa kasashen E4 da ke tarayyar Turai sun nuna shirinsu na cire takunkumi kan Iran bayan cimma yarjejeniyar
- Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake cewa za a sanya hannu kan yarjejeniyar a Switzerland tare da fara ƙarin kwanaki 60 na tattaunawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Shugabannin duniya sun yi maraba da yarjejeniyar da Amurka da Iran suka cimma domin kawo ƙarshen yaƙin da ya ɗauki kusan watanni huɗu a Gabas ta Tsakiya.
A wani mataki da Iran ta ci riba, wasu ƙasashen Turai sun nuna shirinsu na cire takunkumin da suka kakaba wa Tehran idan Iran ta ɗauki matakan da za su takaita shirinta na nukiliya.

Source: Getty Images
CNBC ta wallafa cewa hakan ya biyo bayan yarjejeniyar da Amurka da Iran suka cimma a ranar Lahadi wadda za ta kawo ƙarshen rikicin nan take kuma har abada.
Ribar da Iran ta samu a Turai
A wata sanarwa ta haɗin gwiwa bayan sanar da yarjejeniyar, Birtaniya, Faransa, Jamus da Italiya sun yaba da yarjeneitar, inda suka bayyana ta a matsayin:
“Wata dama ta dawo da zaman lafiya a yankin da kuma daidaita tattalin arzikin duniya.”
Sun kuma bayyana cewa a shirye suke su cire takunkuman da suka kakakabwa Tehran idan Iran ta yi aiki da sharudan da ta amince da su a yarjejeniyar game da nukiliya.
Ƙungiyar ƙasashen nan huɗu, wadda ake kira E4, ta kuma buƙaci a aiwatar da yarjejeniyar cikin gaggawa tare da jaddada cewa:
“Sake buɗe mashigar ruwan Hormuz cikin gaggawa tare da cikakkiyar ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa ba tare da wani sharadi ko takurawa ba yana da matuƙar muhimmanci.”
Martanin shugabannin duniya
Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wani babban ci gaba wajen kawo ƙarshen yaƙin, tare da jaddada cewa mashigar Hormuz za ta cigaba da zama a bude.
Firaministar Japan, Sanae Takaichi, ta ce ƙasarta na maraba da yarjejeniyar a matsayin babban mataki wajen warware matsalar.
Reuters ta wallafa cewa ta bayyana fatan cewa za a aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata, a tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin ‘yanci da aminci a mashigar Hormuz.
Ana sa ran Trump zai gana da shugabannin ƙasashen G7 — Kanada, Faransa, Jamus, Italiya, Japan da Birtaniya — da kuma Tarayyar Turai a taron shekara-shekara da zai fara a Faransa.

Source: Getty Images
Shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, ya taya ɓangarorin da suka yi yaƙin murnar cimma yarjejeniyar, yana mai bayyana ta a matsayin
Trump ya yi yarjejeniya da Iran
A wani labarin, mun kawo muku cewa jami’an Amurka da Iran sun bayyana cewa sun amince da wani tsarin zaman lafiya wanda ake sa ran zai kawo ƙarshen yaƙin da aka yi tsakaninsu.
Ana sa ran yarjejeniyar za ta kawo ƙarshen katangar ruwa da Amurka ta kafa wa Iran, da sake buɗe mashigar ruwan Hormuz da Iran ta toshe.
Pakistan ta ce za a sanya hannu kan yarjejeniyar a makon da muke ciki, wadda za ta kawo ƙarshen yaƙin da Amurka da Isra’ila suka fara a ƙarshen watan Fabrairun 2026.
Asali: Legit.ng


