Bayan Yarjejeniya da Amurka, Shugaban Iran Ya Yi Martani game da Sulhu
- Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian ya yaba yarjejeniyar fahimtar juna da Amurka a matsayin lamari mai tarihi
- Ya ce yarjejeniyar ta nuna murya ta al’umma da ta ki mika 'yancin ta ga barazana ko matsin lamba ta kudiri tsayin
- Yarjejeniyar ta hada da kawo karshen ayyukan soja, tattaunawa kan shirin nukiliya, sassauta takunkumi da sakin dukiyar Iran da aka rike da man fetur
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya yi magana game da sulhu da kasar Amurka a yankin da ake a Gabas ta Tsakiya.
Pezeshkian ya yaba sabuwar yarjejeniyar fahimtar juna da aka kulla tsakanin Iran da Amurka wanda ya kawo karshen yaƙi.

Source: Getty Images
Hakan na cikin wasu sakonni biyu daban-daban da ya wallafa a dandalin sada zumunta na X a yau Alhamis 18 ga watan Yunin 2026.
Shugaban Iran ya magantu kan yarjejeniya da Amurka
Pezeshkian ya bayyana yarjejeniyar a matsayin "tarihi” da kuma sakamakon juriyar kasa da diflomasiyya mai nagarta.
Pezeshkian ya ce takardar da ke kunshe da yarjejeniyar ta nuna muryar al’umma daya da ba ta sayar da daraja da ‘yancinta ga kowace barazana ko matsin lamba.
Ya ce:
“Abin da aka rubuta a yau sakamakon juriya ta kasa, tunani mai kyau na siyasa da diflomasiyya ce."
A cikin wani saƙo na biyu, shugaban Iran ya bayyana yarjejeniyar a matsayin “takarda tarihi da kuma saƙo daga Iran mai ƙarfi.”
“Zaman lafiya zai samu ne ta hanyar mutunta juna."
- In ji Pezeshkian.

Source: Getty Images
Abin da Iran ta sanya a gaba
Pezeshkian ya kara da cewa Iran na ci gaba da jajircewa wajen zaman lafiya a duniya, tare da “kare darajarta, ‘yancinta, ci gabanta da hadin gwiwar yankin.
Wannan bayanin ya biyo bayan sanarwar Tehran da Washington da suka yi kwanan nan kan rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da nufin kawo karshen rikici na watanni da kuma bude tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran da sassauta takunkumi.
Yarjejeniyar ta hada da tanade-tanade kan dakatar da ayyukan soja a fannoni daban-daban na yankin, sassauta takunkumi kan fitar da mai na Iran, sakin kadarorin Iran da aka rike, da kuma tabbatar da ‘yancin zirga-zirga a mashigar tekun Hormuz.
Masana na ganin cewa wannan yarjejeniya za ta kawo karshen yakin tare da farfaɗo da tattalin arzikin duniya da ya fara samun matsala dalilin yakin da ake yi.
Gargadin da Iran ta yi ga Amurka
A baya, mun ba labarin cewa rundunar IRGC ta Jamhuriyar Musulunci a Iran ta yi barazanar kai munanan hare-hare kan sansanonin Amurka da jiragen ruwa.
Kasar Iran ta yi wannan gargadi ne ga kasar idan ta kai hari kan tankokin mai ko jiragen kasuwancin kasar wanda ka iya jawo martani mai zafi.
Rikicin Iran da Amurka tare da Isra’ila ya kara tsananta bayan hare-haren da aka kai tun watan Fabrairu, lamarin da ya haddasa martanin Tehran da rikicin mashigar Hormuz.
Asali: Legit.ng

