Ahmad Yusuf
11845 articles published since 01 Mar 2021
11845 articles published since 01 Mar 2021
Kotun Majistare a jihar Kano ta bayar da umarnin tsare Muhammad Najib Rimin Kebe kan zargin kutse da satar takalma a masallacin Kotunan Norman’s Land.
Kakakin Majalisar dokokin jihar Edo, Blessing Agbebaku, ya yi murabus bayan ‘yan majalisa sun shirya tsige shi, kamar yadda mai taimaka masa ta tabbatar.
Tarayyar Turai ta ware €2.3m ga Najeriya da wasu ƙasashe uku domin yaƙi da annobar kwalara, inda Najeriya za ta samu €1.5m daga cikin jimillar kudin.
Dan takarar jam'iyyar PRP, Donald Duke, ya buƙaci ‘yan adawar Najeriya su binne son zuciya, su haɗa kai domin kayar da APC a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Hukumar kashe gobara ta tabbatar da mutuwar leborori 4 da dalibar Islamiyya daya sakamakon ruftawar wasu gine-gine biyu a kananan hukumomi 2 a Kano.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida, murnar cika shekaru 85, yana yabawa gudunmawarsa ga Najeriya.
Manoma biyar sun mutu bayan wani jirgin ruwa ya kife a Kogin Kudi da ke Katcha, Jihar Neja, yayin da suke kan hanyar zuwa gonakinsu a karshen mako.
Yan takarar shugaban kasa na jam'iyyun Accord, AAC da SDP sun shirya hada maka domin tunkarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na APC a babban zaben 2027.
Gwamna Ademola Adeleke dan kasuwa ne kafin ya tsunduma harkar siyasa, ya je majalisar dattawa gabanin ya samu nasarar zama gwamnan jihar Osun a zaben 2022.
Ahmad Yusuf
Samu kari