"Kun Tona wa Kanku Asiri," Wike Ya Taso Atiku, Peter Obi da Kwankwaso Ana Shirin Zaben 2027
- Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya ayyana manyan jagororin adawar Najeriya a matsayin makaryata
- Wike ya soki manyan jam'iyyun adawa da suka hada da NDC da ADC, yana mai cewa sun gaza bin tafarkin dimokuradiyya a cikin gida
- A cewarsa, wasu daga cikin yan siyasar da suka nemi takarar shugaban kasa a jam'iyyun adawa, sun fito sun tona wa kansu asiri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya yi kakkausar suka ga wasu fitattun ‘yan adawa a Najeriya.
Wike ya caccaki tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso, inda ya zarge su da yaudarar ‘yan Najeriya da ikirarin cewa su ne za su kawo canji a kasar.

Source: Facebook
Wike ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na wata-wata da ya saba gudanarwa a Abuja ranar Litinin, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Ya ce abubuwan da suka faru a zaɓukan fitar da gwani na jam’iyyun adawa sun nuna cewa suna fama da matsaloli.
Wike ya soki jam'iyyun NDC da ADC
Ministan ya mayar da hankali kan NDC da ADC, yana mai cewa rikice-rikicen da suka biyo bayan zaɓukan fitar da gwani na wadannan jam’iyyu sun nuna cewa ba su da cikakken shiri da zai ba su damar jagorantar Najeriya.
A cewarsa, jam’iyyun da suke bayyana kansu a matsayin masu kawo gyara da inganta dimokuraɗiyya sun kasa gudanar da harkokinsu na cikin gida cikin lumana.
Wike ya ce:
“Sun ce su ne masu ceto da za su zo su gyara kasa, amma me ya faru yanzu? NDC ta ce ita ce sabuwar fuskar dimokuraɗiyya.
"ADC kuma ta ce ita ce jam’iyyar da ba ta gurɓata ba, kamar wacce aka haifa a yau. Amma yanzu komai ya lalace.”
Wike ya tabo wasu manyan yan takara
Ministan Abuja ya ce abin mamaki ne yadda NDC ta kasa gudanar da zaɓen fitar da gwani cikin lumana duk da cewa jam’iyyar ba ta da girman wasu manyan jam’iyyu.
A cewar Wike, wasu daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa a jam’iyyun adawa ne da kansu suka fito suka soki yadda aka yi zaben fitar da gwani lamarin da ya nuna cewa akwai tarin matsaloli a cikin gidajensu.

Source: Facebook
Wike ya ce abubuwan da suka faru sun fallasa masu kokarin gabatar da kansu a matsayin masu ceto ko masu gyaran siyasar Najeriya.
Rahoton Vanguard ya tattaro Wike na cewa:
“Wa yake yaudarar wa? Wa zai zo ya gaya wa ‘yan Najeriya cewa shi mai tsafta ne ko kuma mai ceton wannan zamani?” Yanzu ‘yan Najeriya sun fahimci cewa duk makaryata ne. Ba za su ci gaba da yaudarar jama’a ba.”
Wike ya jaddada goyon baya ga Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike, ya nuna goyon bayansa ga tazsrcen Shugaba Bola Tinubu a zaben shekarar 2027 da ke tafe.
Wike ya bayyana cewa Rivers ba ta da wani zaɓi face ta ci gaba da mara wa Shugaba Bola Tinubu baya domin ya yi wa'adi biyu a mulkin Najeriya.
A cewarsa, daga shekarar 2023 zuwa yanzu, Rivers ta samu muƙamai da damammaki masu yawa, saboda haka ya kamata jama'a su nuna godiya ga shugaban ƙasa.
Asali: Legit.ng

