'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Masallaci Ana tsakiyar Sallar Magriba a Kaduna

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Masallaci Ana tsakiyar Sallar Magriba a Kaduna

  • 'Yan bindiga sun kashe mutum 1 tare da sace wasu dama a wani hari da suka kai masallaci ana cikin sallar Magriba a Kaduna
  • Rahotanni sun nuna cewa ana zargin harin na ramuwar gayyar ne bayan sojoji sun ragargaji yan bindigar a kwanakin baya
  • Wani mazaunin yankin mai suna Abdullahi Mustapha ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce maharan sun kai harin ne ana tsaka da sallah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - ‘Yan bindiga sun kai hari wani masallaci da ke kauyen Ungwan Namama a yankin Kaya, karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kashe mutum guda tare da yin garkuwa da wasu masu ibada da ba a tantance adadinsu ba.

Kaduna.
Taswirar jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa maharan sun shiga kauyen ne da misalin karfe 7:30 na yammacin ranar Lahadi, sannan suka nufi masallacin kai tsaye a lokacin da al’umma ke gudanar da sallar Magariba.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace tsohon manjo janar da matarsa a Katsina

Ana zargin harin ramuwar gayya ne

Wata majiya daga yankin, wadda ta nemi a sakaya sunanta saboda dalilan tsaro, ta ce akwai yiwuwar harin ya kasance ramuwar gayya bayan wani samame da sojoji suka kai a yankin kwanakin baya.

A cewarta, jami’an tsaro sun yi nasarar yi wa wasu ‘yan bindiga kwanton bauna a yankin tare da kashe kusan mutum takwas daga cikinsu.

Majiyar ta ce maharan na zargin cewa wasu mazauna kauyen ne suka ba sojoji bayanan sirri game da motsinsu, lamarin da ya fusata su.

“Sun yi zargin cewa mutanen kauyen ne suka sanar da sojoji game da inda suke buya. Wannan ne ya sa suka dawo domin daukar fansa kan al’ummar yankin,” in ji majiyar.

Yan bindiga sun jikkata masallata 5

Rahotanni sun nuna cewa mutum biyar sun samu raunuka daban-daban yayin harin, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

An ce da farko an ba su kulawar gaggawa a yankin kafin daga bisani a garzaya da su zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Zariya domin ci gaba da jinya.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: 'Yan bindiga sun bude wa mutane wuta bayan kammala sallar Juma'a

Wani mazaunin yankin mai suna Abdullahi Mustapha ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce maharan sun kai harin ne a daidai lokacin da mutane ke gudanar da salla a masallaci.

“Sun iso da misalin karfe 7:30 na yamma lokacin da mutane ke sallar Magariba. Sun kashe mutum guda, sun jikkata biyar sannan suka tafi da wasu mutane da dama,” in ji shi.
Gwamna Uba Sani.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani a fadar gwamnati Hoto: Uba Sani
Source: Twitter

Wani babban jami’in tsaro wanda shi ma ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da aukuwar harin.

Ya ce har yanzu hukumomi na ci gaba da tattara bayanai domin tantance yawan wadanda suka rasa rayukansu da kuma wadanda aka yi garkuwa da su.

Jami'an tsaro sun cafke dan bindiga a Kaduna

A wani labarin, kun ji cewa dakarun rundunar Operation Fansan Yamma sun kama wani mutum da ake zargin dan bindiga ne a jihar Kaduna.

An cafke Ibrahim Adamy ne yayin wani samame na binciken ababen hawa a karamar hukumar Birnin Gwari da ke Kaduna a yankin Arewa maso Yamma.

Majiyoyin sun ce yayin binciken da aka yi masa, an kwato mujallar bindigar AK-47 guda daya, wayoyin hannu uku, tabar wiwi da wasu kayayyaki daga hannunsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262