Yadda Hukumar Bogi Ta So Tatso Naira Biliyan 50 Kafin a Yi Ram da Shugaban Karya
- Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin a gaggauta kama George Buchi Nwabueze mai jagorantar hukumar karya
- Kafin hakan ta faru, hukumar ta ci damarar shirya wani taron kasa-da-kasa da zai jawo wa Najeriya makudan biliyoyi
- Hukumar ta ce ta yi nufin bunkasa tattalin Najeriya, karfafa wa masu hada kaya a Najeriya da kuma tallata kayan a duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - An tono shirin da ofishin Made in Nigeria Project da aka kirkiro domin karfafa kayan gida yake yi kafin labari ya canza a watan nan.
Wannan hukuma ta bogi tana da nufin shirya wani taro na kasa da kasa wanda ya yi nufin samowa Najeriya fiye da Naira biliyan 50.

Source: Getty Images
Hukumar bogi na shirye-shiryen nemo N50bn
Daily Trust ta rahoto cewa hakan ta faru ne kafin Gwamnatin tarayya ta juya wa hukumar baya, tana cewa ba ta san da zaman ta ba.

Kara karanta wannan
Biza: Amurka ta gano makircin da ake shiryawa, ta aiko da muhimmin saƙo ga yan Najeriya
Bayanan da aka samu a shafin hukumar na yanar gizo ya nuna cewa tana yunkurin yin taro da nufin karfafa masana’antun Najeriya.
An nuna cewa taron ya yi nufin ya kunshi baja-kolin kaya, shirya majalisun kasuwanci, yarjejeniyar zuba hannun jari da kasashen waje.
Dama an ji yadda aka rika aika takarda zuwa ga gwamoni domin neman kudi da sunan shirya taro a waje.
Kasashen da hukumar bogin ta fake da su
Kasashen ketaren da aka yi niyyar hada-kai da su wajen cin ma wannan manufa su ne Qatar, Kuwait, China, Hong Kong da Brazil.
Hukumar ta ce yunkurin zai kawo fiye da Naira biliyan 50 cikin tattalin arzikin Najeriya. Ba a san ko shirin gaskiya ne ko kuma damfara ba.
Alherin bai tsaya nan ba, za a inganta kasuwanci na cikin gida, a karfafi kayan da ake yi a Najeriya kuma a tallata su gaban kasashen duniya.

Kara karanta wannan
Atiku ya ɗauki zafi, ya sake fallasa abin da yan Najeriya ba su sani ba kan tallafin man fetur
Abin da aka yi niyya shi ne a fara tallata wannan yunkuri a Qatar, Kuwait da China a yanzu.
Daga nan kuma sai a shiga tallata kayan da aka hada a Najeriya a biranen kasashen Brazil da Hong Kong zuwa karshen shekarar nan.
Lambar Sakataren gwamnatin tarayya ya kara fitowa
Hukumar ta yi ikirarin cewa duk wannan yana karkashin sashen harkokin tattalin arziki a Ofishin sakataren gwamnatin tarayya.
Duk abin da yake faruwa, an ji cewa sakataren gwamnatin tarayya bai ce uffan ba har zuwa yau duk da zargin da ake jifarsa da shi.
A Yunin 2023 Bola Tinubu ya amince da nadin tsohon gwamnan Benuwai, Sanata George Akume a matsayin sakatare na gwamnatinsa.
Idan da ta ci nasara, hukumar ta yi niyyar gayyato masu kudi daga kasashen waje ta yadda za su shiga yarjejeniya da mutanen Najeriya.
Wannan zai ba kamfanonin kasar nan damar fita da kayan su zuwa kasashen waje idan har ta tabbata da gaske za a shirya taron.

Source: Getty Images
Karin hukumar bogi da gwamnati ta gano

Kara karanta wannan
Ganin sunan korarriyar minista da mutanen EFCC a kwamitin neman zabe ya jawo surutu
An ji labari ICPC ta bayyana cewa ta gano wata sabuwar hukumar da ba san da zaman ta ba, tana aiki ba tare da izinin shugaban kasa ba.
An dakatar da manyan sakatarorin gwamnatin tarayya guda uku sakamakon binciken da aka gudanar kan wannan hukuma guda ta bogi.
George Buchi Nwabueze shi ne jagoran shirin na kasa kuma babban darektan hukumar wanda tuni shugaban kasa ya bada umarnin a kama shi.
Asali: Legit.ng