INEC Ta Fara Bincike, Ta Bankado Bayanai kan Hotunan da Hadimin Ministan Abuja Ya Wallafa
- Hukumar INEC ta yi martani kan zargin fallasa bayanan jarumin Nollywood, Emeka Ike, wanda ya fito takarar dan Majalisa a Abuja
- Mai magana da yawun ministan Abuja, Lere Olayinka ne ya wallafa bayanan rijistar jarumin, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce mai zafi
- INEC ta bayyana cewa ta fara gudanar da bincike kuma ta fara gano yadda aka samu bayanan daga shafinta na gudanarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yi karin haske kan takaddamar da ta taso bayan bayyanar wasu bayanan rajistar zabe da suka shafi wani dan siyasa a kafafen sada zumunta.
Lamarin ya samo asali ne bayan mai magana da yawun Ministan Abuja, Nyesom Wike, wato Lere Olayinka, ya wallafa wasu bayanai da suka shafi fitaccen jarumin Nollywood, Emeka Ike.

Kara karanta wannan
Shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, Chinda ya yi murabus daga mukaminsa

Source: Facebook
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa Emeka Ike ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar AMAC/Bwari a Abuja karkashin jam'iyyar NDC.
Yadda hadimin Wike ya tada kura
An ce Olayinka ya yi tsokaci kan matakin da Emeka Ike ya dauka na sauya rumfar zabensa daga jihar Imo zuwa Babban Birnin Tarayya a ranar 15 ga watan Mayu.
A yayin wallafa sakon nasa, ya hada da wasu hotuna guda biyu da suka nuna bayanan rajistar zaben jarumin.
Wannan mataki ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama suka fara tambayar yadda aka samu damar fitar da irin wadannan bayanai na sirri daga shafin INEC.
Wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun yi zargin cewa hotunan sun fito ne daga shafin gudanarwar cikin gida na hukumar zabe.
Wane mataki INEC ta dauka?
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a Facebook, hukumar INEC ta bayyana cewa ta dauki lamarin da matukar muhimmanci.
Hukumar ta ce nan take ta fara gudanar da cikakken bincike domin gano hakikanin abin da ya faru da kuma yadda aka samu bayanan.
INEC ta bayyana cewa yayin gudanar da rajistar masu kada kuri'a (CVR), jami'an rajista na musamman suna samun damar shiga wasu sassan tsarin domin yin rajista, canja wurin rajista da sabunta bayanan masu zabe.
Sai dai ta jaddada cewa irin wannan damar tana da iyaka kuma ana amfani da ita ne kawai wajen gudanar da aikin hukuma.

Source: Facebook
Da gaske an yi wa INEC kutse?
Hukumar ta ce sakamakon binciken farko ya nuna babu wani kutse daga waje da aka yi wa shafin adana bayanai ko tsarin fasahar sadarwar ta INEC.
A cewarta, bayanan da aka wallafa an samu su ne ta hanyar amfani da sahihan bayanan shiga da aka bai wa wasu jami'ai da ke aikin rajistar masu kada kuri'a, amma aka fitar da su ba tare da izini ba.
INEC ta kara da cewa binciken da take yi ya gano asusun da aka yi amfani da shi wajen samun bayanan, kuma an fara tambayar jami'an da abin ya shafa.
Hukumar INEC ta daukaka kara
A wani labarin, kun ji cewa hukumar INEC ta daukaka kara kan hukuncin da ya soke duka wa'adin da ta sanya wa jam'iyyun siyasa a jadawalin babban zaben 2027.
Lauyan INEC, Alex Izinyon (SAN), wanda ya shigar da kara a gaban kotun daukaka kara ta Abuja, ya nemi a jingine hukuncin da babbar kotun tarayya ta yi.
Baya ga neman a soke hukuncin, babban lauyan ya kuma buƙaci kotun ta dakatar da aiwatar da hukuncin har sai an kammala sauraron ɗaukaka ƙarar.
Asali: Legit.ng

