Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Tsohon Alkalin Kotun Koli, Umaru Kalgo, Ya Rasu

Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Tsohon Alkalin Kotun Koli, Umaru Kalgo, Ya Rasu

  • Tsohon Alkalin Kotun Ƙoli, Umaru Atu Kalgo, ya yi bankwana da duniya bayan ya yi fama da doguwar rashin lafiya
  • Marigayin ya shafe kusan shekaru 50 yana aikin shari’a, inda ya yi aiki a Kotun Ɗaukaka Ƙara da Kotun Ƙoli ta Najeriya
  • Tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga iyalan marigayin da fannin shari’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Al’ummar fannin shari’a da Najeriya baki ɗaya sun shiga jimami sakamakon rasuwar tsohon Alkalin Kotun Ƙoli, Mai Shari’a Umaru Atu Kalgo, JSC, CON.

Marigayin, wanda ya kasance fitaccen masani kan shari’a kuma dattijon ƙasa, ya rasu ne da misalin ƙarfe 3:00 na safiyar Talata, 25 ga watan Agustan 2026 bayan fama da doguwar rashin lafiya.

Mai sharia Umaru Kalgo ya rasu
Marigayi Umaru Atu Kalgo da Sanata Aminu Waziri Tambuwal Hoto: @AWTambuwal
Source: Twitter

An binne shi a Sokoto

Jaridar The Sun ta ce wani mazaunin Kalgo da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa an yi wa marigayin jana’iza sannan aka binne shi da misalin ƙarfe 2:30 na rana a Sokoto, bisa tsarin jana’izar Musulunci.

Kara karanta wannan

Gwamna ya halarci taron ƙungiyar Izala, ya ce tallafin Tinubu na isa ga talakawan Najeriya

Rasuwarsa ta kawo ƙarshen rayuwar wani fitaccen ɗan shari’a wanda ya sadaukar da kusan shekaru 50 wajen yi wa shari’a, adalci da tsarin shari’ar Najeriya hidima.

Tarihin rayuwar mai shari’a Umaru Kalgo

An haifi Umaru Atu Kalgo a ranar 12 ga Mayu, 1937, a garin Kalgo na Jihar Kebbi, wadda a lokacin take ƙarƙashin tsohuwar Jihar Arewa maso Yamma.

Ya yi karatunsa na firamare a Elementary School Kalgo, sannan ya halarci Middle School Sokoto da Middle School Birnin Kebbi. Daga bisani ya yi karatu a Government College Zaria tsakanin shekarar 1953 zuwa 1958.

Umaru Atu Kalgo ya kuma yi karatun shari’a a Institute of Administration na Ahmadu Bello University da ke Zaria, Council of Legal Education da College of Law Holborn a London, da kuma Nigerian Law School da ke Legas.

A watan Fabrairun 1988 aka naɗa Umaru Atu Kalgo a matsayin Alkalin Kotun Ɗaukaka Ƙara. Daga bisani, a ranar 25 ga Nuwamba, 1998, aka ɗaga shi zuwa Kotun Ƙoli ta Najeriya, inda ya yi aiki a matsayin Alkalin Kotun Ƙoli har zuwa lokacin da ya yi ritaya a watan Mayun 2007, bayan ya cika shekaru 70.

Kara karanta wannan

Farfesa ya ɗauko tarihi, ya fadi yadda rasuwar Umaru Musa Yar'adua ta illata Najeriya

Tambuwal ya yi masa ta’aziyya

Tsohon Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana alhininsa kan rasuwar tsohon Alkalin Kotun Ƙolin.

A cikin saƙon ta’aziyyarsa da ya wallafa a shafinsa na X, Tambuwal ya ce rasuwar Kalgo babban rashi ne ga iyalansa, al’ummar Jihar Kebbi, bangaren shari’a da kuma Najeriya baki ɗaya.

Ya ce rayuwar marigayin ta kasance sadaukarwa wajen neman adalci, kare bin doka da yi wa ƙasa hidima.

Ya taimaka wajen bunƙasa dokokin Najeriya

Tambuwal ya bayyana cewa Kalgo ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tsarin shari’a a Najeriya ta hanyar hukuncin da ya yanke da kuma gudummawar da ya bayar kan dokokin kundin tsarin mulki, shari’ar farar hula da laifuka.

Tambuwal ya ce tarihin Kalgo ya kasance na ilimi, ƙwarewa, gaskiya da jajircewa wajen tabbatar da adalci.

Ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya karɓi kyawawan ayyukansa, Ya kuma ba shi Aljannatul Firdaus.

Tambuwal ya kuma roƙi Allah Ya bai wa iyalan marigayin da sauran waɗanda rasuwar ta shafa ƙarfin jure wannan babban rashi.

Kara karanta wannan

APC: 'Dalilin Atiku na yin alkawarin dawo da tallafin man fetur idan an zaɓe shi'

Atu Kalgo ya bar duniya
Marigayi Umaru Atu Kalgo, tsohon alkalin Kotun Koli Hoto: @AWTambuwal
Source: Twitter

Fitaccen jarumi, Hassan Ogogo, ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Najeriya, Taiwo Hassan, wanda aka fi sani da Ogogo, ya rasu.

Taiwo Hassan ya kasance daya daga cikin fitattun jaruman masana’antar fina-finan Najeriya, musamman a bangaren fina-finan harshen Yarbanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng