Gwamna Abba Ya Kadu da Allah Ya Yi wa Tsohon Kwamishina Rasuwa a Jihar Kano

Gwamna Abba Ya Kadu da Allah Ya Yi wa Tsohon Kwamishina Rasuwa a Jihar Kano

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi alhinin rasuwar tsohon kwamishinan albarkatun ruwa da raya karkara, Dr. Mahmud Baffa Yola
  • Rahotanni sun nuna cewa tsohon kwamishinan ya rasu ne bayan fama da doguwar rashin lafiya, lamarin da ya ga girgiza Gwamna Abba
  • Abba ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin, yana mai bayyana cewa rasuwar Dr. Mahmud Baffa babban rashi ne ga Kano baki daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Tsohon Kwamishinan Albarkatun Ruwa da Raya Karkara na jihar Kano, Dr. Mahmud Baffa Yola ya rasu bayan jinya mai tsawo.

Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana matuƙar alhini da kaɗuwa bisa rasuwar tsohon Kwamishinan, Mahmud Baffa Yola, wanda ya rasu bayan fama da doguwar rashin lafiya.

Gwamna Abba.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya daga hannu yana addu'a Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Asabar, 30 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

Gwarzo: "Adadin Kanawa da ake hallakawa a gwamnatin Abba ya fara yawa"

Gwamna Abba ya fadi alherin Dr. Mahmoud

Gwamna Abba ya bayyana marigayi Mahmud Yola a matsayin jajirtaccen ma’aikacin gwamnati wanda ya bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen bunƙasa harkokin albarkatun ruwa da ci gaban yankunan karkara a jihar Kano.

A cewarsa, marigayin ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’umma hidima cikin gaskiya, ƙwarewa da kuma kishin jama’a ba tare da gajiyawa ba.

Gwamnan ya ce rasuwar tsohon kwamishinan babban gibi ne ga jihar Kano, la’akari da irin rawar da ya taka wajen tsara manufofi da shirye-shiryen da suka taimaka wajen inganta rayuwar al’umma, musamman mazauna karkara.

Gwamna Abba ya ce:

"Mun yi rashin mutum mai kishin al’umma wanda ya sadaukar da lokacinsa da ƙarfinsa wajen ci gaban jama’a. Gudunmawar da ya bayar wajen hidimtawa jiharmu za ta ci gaba da kasancewa cikin tarihi kuma ba za a manta da ita ba."
Kano.
Taswirar jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Gwamna ya yi addu'a ga marigayin

Gwamna Abba Kabir ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayi Dr. Mahmoud, abokansa, masu hulɗa da shi da kuma daukacin al’ummar jihar Kano bisa wannan babban rashi da aka yi.

Kara karanta wannan

Martanin Kwankwaso bayan samu tikitin takarar mataimakin Peter Obi a NDC

Ya kuma yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdausi, tare da bai wa iyalansa da masoyansa juriyar ɗaukar wannan babban rashi da ya same su.

Gwamna Abba ya yi ta'aziyyar malamin BUK

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya mika sakon ta'aziyya bisa rasuwar babban malami a jami'ar BUK, Dr.Musa Adamu Labaran.

Marigayin wanda ke aiki a Tsangayar Sadarwa ta Jami'ar Bayero da ke Kano (BUK) ya riga mu gidan gaskiya ne a jiya Litinin da ta gabata bayan gajeruwar rashin lafiya.

Abba Kabir ya ƙara da cewa Dr Labaran ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa, bincike da horas da ɗalibai da ƙwararru da dama, inda ya bar tarihi na ƙwarewa, gaskiya da hidima ga bil’adama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262