2027: Babachir Lawal Ya Rikita Lissafin Atiku Abubakar, Ya Fice daga Jam'iyyar ADC

2027: Babachir Lawal Ya Rikita Lissafin Atiku Abubakar, Ya Fice daga Jam'iyyar ADC

  • Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya zargi ADC da magudi a zabukan fitar da gwani domin fifita Atiku Abubakar
  • Babachir ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar ADC, yana mai cewa ba zai ci gaba da zama a wurin da babu adalci ba
  • Ya bayyana ra'ayinsa cewa duk da matsalolin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke fuskanta, shugaban kasar na iya fin Atiku zama alheri ga Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar ADC a hukumance.

Babachir Lawal ya kuma yi zargin cewa zaɓukan fitar da gwani da jam’iyyar ADC ta gudanar sun kasance cike da magudi da rashin adalci.

Babachir Lawal.
Tsohon sakataren gwamnatin Najeriya, Babachir Lawal Hoto: Babachir Lawal
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Babachir ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 1 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

"Kun tona wa kanku asiri," Wike ya taso Atiku, Peter Obi da Kwankwaso ana shirin zaben 2027

Ya ce abin da ya gani yayin gudanar da zaɓen fitar gwani ya sa ya rasa amincewa da tsarin dimokuraɗiyyar cikin gida na jam’iyyar ADC

Babachir ya zargi Atiku da cin moriyar magudi

Tsohon SGF din ya yi ikirarin cewa an karkatar da sakamakon zaɓen fitar da gwani domin fifita tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da wasu da ke kusa da shi a siyasa.

A cewarsa, a wuraren da aka gudanar da zaɓe, an sauya sakamakon da aka samu domin bai wa wasu takamaiman mutane nasara.

Babachir Lawal ya raba gari da ADC

A kalamansa, Babachir ya ce:

"Na yanke shawarar ficewa daga ADC saboda zaɓukan fitar da gwani da aka gudanar a dukkan matakai sun kasance cike da magudi domin fifita Kachalla Atiku Abubakar.
"An sauya sakamako domin amfanin Atiku da mutanensa. Ko inda aka bari aka gudanar da zaɓe, waɗanda suka yi nasara an cire su tare da maye gurbinsu da wasu daga cikin tawagarsa. A hakikanin gaskiya, abin kunya ne kuma wasan kwaikwayo ne."

Babachir ya ce daya daga cikin manyan dalilan da suka sa ya fice daga ADC shi ne rashin son kasancewa cikin abin da ya kira "injin magudin zaɓe" na Atiku a babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

'Jirgi marar matuki zan nada': Sowore kan wanda zai ba ministan tsaro idan ya ci mulki

Atiku Abubakar.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar a taron jam'iyyar ADC Hoto: @atiku
Source: Facebook

Babachir Lawal zai yaki takarar Atiku

A cewarsa, ci gaba da zama cikin jam’iyyar zai sanya shi cikin wani tsari da ba ya goyon baya, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

A cikin sanarwar, Babachir ya bayyana ra'ayinsa cewa duk da matsalolin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke fuskanta, shugaban kasar na iya zama mafi alheri ga Najeriya idan aka kwatanta da Atiku Abubakar.

"Zan koma gona ta a kauye na ɗan lokaci, amma zan ci gaba da bibiyar siyasa da kuma tattaunawa da masu kishin kasa domin ganin an hana wannan tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Atiku kusantar Aso Rock," in ji shi.

Atiku ya maida martani ga Wike

A wani rahoton, kun ji cewa 'dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ragargaji Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike kan zaben 2027.

Tun farko, Wike ya yi ikirarin cewa Atiku ba zai samu kaso 10 cikin 100 na yawan kuri'un da jama'ar jihar Ribas za su kada a zaben shugaban kasar 2027.

Da yake martani, Atiku ya ce masu kada kuri’a a jihar Rivers suna da hikima da wayewar kai da za su yanke hukuncin wanda za su zaba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262