Abu Ya Girma: Shirin Atiku na Dawo da Tallafin Mai na Iya Tsorata Wasu Yan Kasashen Waje
- Kungiyar IMPI ta ce shirin Atiku Abubakar na dawo da tallafin man fetur na iya tsoratar da masu zuba jari daga ƙasashen waje
- Omoniyi Akinsiju ya ce tsarin na iya rage kuɗaɗen shiga Asusun Tarayya tare da ƙara matsin lamba kan tattalin arziki
- Kungiyar ta yi gargadin cewa kayyade farashin man fetur na iya haifar da ƙarancin mai a yankunan karkara da ƙara hauhawar farashin ababen hawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Wata ƙungiyar nazarin manufofi, Independent Media and Policy Initiative (IMPI), ta ce dawo da tallafin lan fetur zai iya tsorata yan kassshen waje da ke zuba jari a Najeriya.
Ta ce kudurin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, na dawo da tallafin man fetur zai iya zama babbar illa da tsoratarwa ga masu zuba jari daga ƙasashen waje.

Source: Facebook
Ƙungiyar ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da shugabanta, Dr Omoniyi Akinsiju, ya fitar a Abuja ranar 25 ga Agusta, 2026, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Me IMPI ta hango game da shirin Atiku?
Akinsiju ya ce shirin farfaɗo da tattalin arzikin da Atiku ya gabatar, wato Atiku Economic Recovery Plan (AERP), ya ƙunshi tsarin da zai karkata tallafi daga shigo da man fetur zuwa samar da shi a cikin gida.
Ya ce tsarin zai kuma sauya hanyar bayar da tallafin daga ’yan kasuwa zuwa matatun man fetur na cikin gida, kamar yadda Daily Post ta kawo.
A cewarsa, shirin zai buƙaci matatun man gwamnati da masu zaman kansu da suka cancanta su samu ɗanyen mai daga cikin gida kan rangwamen farashi.
Sai dai ya ce za a bai wa matatun damar samun ɗanyen man mai rahusa ne kawai idan sun amince su mayar da cikakken rangwamen ga yan Najeriya da ke amfani da man fetur.

Kara karanta wannan
Batun dawo da tallafin mai ya tada hankalin shugaban APC na ƙasa, ya tura tambaya 1 ga Atiku
Akinsiju ya bayyana wannan tsari a matsayin mai rikitarwa, yana mai cewa zai tilasta wa kamfanonin kasuwanci kamar NNPC Limited da matatun mai masu zaman kansu bin wasu ƙa’idojin farashi da gwamnati ta tsara.
Ta yaya shirin zai shafi masu zuba jari?
Shugaban IMPI ya ce shirin Atiku zai iya aika saƙo ga kasuwannin duniya cewa Najeriya ba ta da tabbas wajen aiwatar da manufofin tattalin arziki.
Ya ce hakan na iya sa masu zuba jari na ƙasashen waje su ja da baya, tare da dakile wasu manyan ayyukan haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

Source: Getty Images
Akinsiju ya ce irin wannan sauyin manufofi na iya shafar samun kuɗin gudanar da wasu muhimman ayyukan more rayuwa da kuma rage samarwa da haɓakar tattalin arzikin ƙasa.
An bukaci Tinubu ya dawo da tallafi
A wani rahoton, kun ji cewa jigo a APC, Jonathan Vatsa, ya goyi bayan kuma dan takarar shugaban kasaNna ADC, Atiku Abubakar, kan batun dawo da tallafin mai.
Ya ce cire tallafin man fetur bai kawo wata fa’ida ga talakawa ba, illa kara jefa masu karamin karfi cikin matsalar tattalin arziki.
Ya bukaci Shugaba Tinubu ya sake tunani kan manufar cire tallafin tare da daukar matakan da za su rage wa ’yan Najeriya nauyin tattalin arzikin da suke fuskanta.
Asali: Legit.ng
