Shehu Sani Ya Saba da Atiku, Ya Bayyana Babbar Matsalar da Dawo da Tallafin Fetur
- Shehu Sani ya bayyana alkawarin Atiku na dawo da tallafin man fetur a matsayin yaudara da kuma manufar da ba za ta dore ba
- Tsohon Sanatan ya bukaci gwamnati ta mayar da hankali kan gyaran matatun mai da tace danyen mai a cikin Najeriya
- Sani ya bayyana goyon bayansa ga sake zaben Tinubu tare da bukatar ‘yan siyasa su guji amfani da kabilanci da addini a zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana alkawarin tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, na dawo da tallafin man fetur idan ya lashe zaben 2027 a matsayin “yaudara”.
Shehu Sani ya ce Najeriya ba za ta iya komawa tsarin tallafin man fetur da ya ce ya jawo kashe tiriliyan naira tare da kara matsalolin cin hanci da fasa-kwaurin man fetur ba.

Kara karanta wannan
Batun dawo da tallafin mai ya tada hankalin shugaban APC na ƙasa, ya tura tambaya 1 ga Atiku

Source: Facebook
Ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja, inda ya bukaci shugabannin siyasa su nemi hanyoyin da za su farfado da tattalin arzikin kasa maimakon komawa tsohon tsarin tallafin, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Ya ce tallafin fetur ya jawo asarar kudi
Shehu Sani ya ce Najeriya ta kashe tsakanin Naira tiriliyan 3 zuwa 4 wajen tallafa wa man fetur, yana mai cewa irin wannan tsarin ba zai dore ba ga kasa mai arzikin man fetur.
“Iya ganina, duk dan takarar da ya cancanci shugabanci bai kamata ya mayar da mu wannan zamanin ba,” in ji shi.
Ya kuma yi zargin cewa an taba amfani da tsarin tallafin wajen karkatar da kudaden gwamnati da sunan shigo da man fetur cikin kasar.
A cewarsa, wasu daga cikin man da aka tallafa wa farashinsa ana safararsa zuwa kasashen makwabta, inda ake sayar da shi kan farashi mafi tsada, lamarin da ke hana Najeriya amfana da kudaden da take kashewa wajen tallafin.

Kara karanta wannan
Zance ya ƙare, Peter Obi ya bayyana matsayarsa kan batun dawo da tallafin man fetur a Najeriya
Shehu Sani ya bukaci a gyara matatun mai
Tsohon sanatan ya ce maimakon a dawo da tallafin, kamata ya yi gwamnati ta mayar da hankali wajen gyara matatun man Najeriya da tabbatar da cewa ana tace danyen man kasar a cikin gida.
Ya tambayi dalilin da ya sa Najeriya ke ci gaba da fitar da danyen mai, sannan ta shigo da tataccen man fetur daga kasashen waje tare da amfani da kudaden kasashen waje wajen tallafa masa.
Shehu Sani ya ce duk dan siyasar da ya yi alkawarin gyara matatun mai domin Najeriya ta daina dogaro da shigo da man fetur zai yi magana mai ma’ana.
‘Dawo da tallafin ba zai rage farashi ba’
Shehu Sani ya amince cewa cire tallafin man fetur ya jefa ‘yan Najeriya cikin matsanancin hali, amma ya ce dawo da tsohon tsarin ba shi ne mafita ba.
“Dawo da tallafin ba zai rage farashin kayayyaki ba. Zai kawai dagula zaman lafiyar tattalin arzikin kasar ne.” in ji shi.

Kara karanta wannan
Bayan abubuwa sun ɗauki zafi, an fito da gaskiyar shirin Atiku na dawo da tallafin mai a Najeriya
Ya bukaci gwamnatin tarayya ta sanya “tausayi da jin tausayin jama’a” cikin sauye-sauyen tattalin arzikin da take aiwatarwa.

Source: Facebook
Shehu Sani ya yi wa Davido martani
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi watsi da kiran da fitaccen mawaki Davido ya yi.
Sanata Shehu Sani ya yi watsi da kiran na Davido na neman Shugaban Amurka Donald Trump da kasashen duniya su sanya ido kan zaben gwamnan jihar Osun.
Asali: Legit.ng