Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya Sun Yi Watsi da Tayin N100,000 a Matsayin Mafi Karancin Albashi
- Ana ci gaba da sukar tayin gwamnonin Najeriya na kara mafi karancin albashin ma'aikatan gwamnati daga N70,000 zuwa N100,000
- Kungiyar ma'aikatan gwamnatin tarayya (FWF) ta yi watsi da tayin gwamnonin, tana mai cewa adadin bai dace da halin da ma'aikata ke ciki ba
- FWF ta kuma bai wa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu wa'adin wata guda ya magance duk wani nau'in matsalar tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Kungiyar ma'aikatan gwamnatin tarayya (FWF) ta yi watsi da shirin karin mafi karancin albashi zuwa N100,000.
Kungiyar ta bayyana cewa adadin bai dace da halin matsin rayuwa da ma’aikatan Najeriya ke ciki ba.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa kungiyar FWF ta bayyana hakan ne a wani taro na jin ra’ayi da ta gudanar kan matsalolin tsadar rayuwa da rashin tsaro a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan
Dattawan Kwara sun yi barazana da 2027 bayan kashe masu mutum 1200 a mulkin Tinubu
Halin da ma'aikatan gwamnati ke ciki
A cewarta, ma’aikatan gwamnatin tarayya na fama da karancin albashi, bashin hakkoki da gwamnati ta ki biyansu da kuma tabarbarewar tsaro.
FWF ta ce aiwatar da mafi karancin albashin N70,000 bai kawo saukin da ake tsammani ba, domin bai warware matsaloli sa dawainiyar ma’aikata ba.
Ta kuma yi zargin cewa karin albashin da aka yi bai wadatar ba, yayin da wasu hakkoki da gwamnati ta yi alkawarin biya har yanzu ba a biya su ba.
FWF ta yi fatali da tayin N100,000
Kungiyar ta soki shawarar karin albashi zuwa N100,000 da wasu gwamnoni ke goyon baya, tana mai cewa adadin ba zai iya zama albashin da zai wadatar da ma’aikaci ba a halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.
“Muna yin Allah wadai da wannan shawara kuma muna watsi da ita baki daya,” in ji kungiyar FWF.
FWF ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki, tsadar man fetur, faduwar darajar Naira da karin kudin wutar lantarki sun kara jefa ma’aikata cikin mawuyacin hali.
Haka kuma kungiyar ta nuna damuwa kan matsalar rashin tsaro, tana mai cewa ma’aikata da sauran ‘yan kasa na ci gaba da fadawa hannun masu garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka.
Kungiyar ta bukaci Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) da TUC su ayyana yajin aiki na sai baba-ta-gani domin matsa wa gwamnati lamba ta magance matsalolin da ake fuskanta.

Source: Getty Images
Kungiyar FWF ta ba Tinubu wa'adin wata 1
FWF ta kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta biya dukkan basussukan hakkokin ma’aikata tare da kirkiro alawus na tsadar rayuwa domin rage radadin halin da ake ciki, cewar rahoton Punch.
A karshe, kungiyar ta bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu wa’adin kwanaki 30 da ya dauki matakan gaggawa wajen magance matsalar rashin tsaro, kashe-kashe, garkuwa da mutane da kuma tsadar rayuwa.
Wani ma'aikacin gwamnati, Nura Ahmad Aliyu ya ce za su suba ido su ga sabon kafi karancin albashin da gwamnatin tarayya za ta yi, yana mai jaddada cewa N100,000 ta yi kadan.
Da yake bayyana ra'ayinsa ga wakilin Legit Hausa, Nura ya ce ma'aikata na fuskantar wahala da tsadar rayuwa, ta yadda ba su iya daukar dawainiyar da ke kansu.
A cewarsa, wani kalubale da ya kamata a warware shi ne batun aiwatar da tsarin karin albashin idan an cimma matsaya, yana mai kafa hujja da abin da ya faru bayan an amince da N70,000.
NLC ta bukaci a fara biyan ma'aikata N1m
A baya, kun ji cewa kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC) ta yi fatali da yunkurin gwamnoni na kara mafi karancin albashin ma'aikata zuwa N100,000.
NLC ta ce idan aka yi la'akari da hauhawar farashi, ƙarin kuɗin wutar lantarki da tsadar man fetur, ma'aikata sun cancanci a biya albashin Naira miliyan 1 mafi karanci.
Ta yi nuni da cewa kuɗaɗen shiga da gwamnatoci ke samu a yanzu sun karu idan aka kwatanta da shekarun baya, don haka babu wani dalili da zai hana inganta walwalar ma’aikata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

