Sojojin Amurka Sun Kuma Kawo Farmaki Najeriya, An Kashe Manyan Yaran Abu Mainok 3

Sojojin Amurka Sun Kuma Kawo Farmaki Najeriya, An Kashe Manyan Yaran Abu Mainok 3

  • Wasu manyan kwamandojin kungiyar ta'addanci ta ISWAP uku sun bakunci lahira yayin da sojojin Amurka da na Najeriya suka rutsa su a Borno
  • An ruwaito cewa wadanda aka kashe na da kusanci da kasurgumin dan ta'addan nan, Abu Bilal al-Minuki, wanda dakaru suka hallaka a watan Mayu
  • Majiyoyi sun bayyana cewa an kashe fitattun kwamandojin kungiyar yan ta'addan, ciki har da Abubakar Buduma, jagoran yankin Kirta Wulgo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno, Nigeria - Sojojin Najeriya da na Amurka sun yi nasarar kashe wasu manyan kwamandojin kungiyar ISWAP uku da ke cikin yaran marigayi shugaban kungiyar, Abu-Bilal al-Minuki (Abu Mainok).

An kashe al-Minuki ne a wani harin sama da aka kai maboyarsa a yankin Tafkin Chadi, lamarin da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar, sannan Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar da shi a watan Mayu.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda fiye da 20 sun bakunci lahira da sojojin Amurka suka sake kawo dauki Najeriya

Sojoji.
Dakarun sojojin Najeriya suna tsakiyar aiki a Arewa maso Gabas Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

A rahoton da ya wallafa a X, fitaccen mao sharhi kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya tabbatar da kashe hatsabiban 'yan ta'addan uku yau Litinin.

Kwamandojin ISWAP 3 da aka kashe

Ya ce majiyoyin tsaro sun bayyana cewa wadanda aka kashe sun hada da Abu Huraira, Ba Yuram da Mallam Haruna, wadanda ake kallon su a matsayin manyan jagororin ISWAP wajen kai hare-hare, samar da kayan aiki da kuma tsaro.

Rahotanni sun nuna cewa Abu Huraira shi ne jagoran yankin Tumbun Mota kuma surukin Abbor Mainok, daya daga cikin fitattun shugabannin kungiyar.

Ana zarginsa da tsara hare-hare da kuma kula da mayakan ISWAP da ke aiki a yankin Tumbun Mota da kewaye.

Yadda kwamandojin ISWAP suke aiki

Ba Yuram kuwa na daga cikin manyan kwamandojin da ke da alhakin samar da makamai, kayan aiki, jigilar kayayyaki da kuma kula da hanyoyin samar wa kungiyar ISWAP kayayyakin yaki a yankunan Tafkin Chadi.

Kara karanta wannan

"Kun tona wa kanku asiri," Wike ya taso Atiku, Peter Obi da Kwankwaso ana shirin zaben 2027

Sai kuma na ukunsu, Mallam Haruna, wanda bayanai suka nuna shi ne mai tsaron lafiyar Abbor Mainok kuma babban jami’in tsaro na kungiyar.

Ana zarginsa da tsara yadda ake kare shugabannin kungiyar tare da kula da zirga-zirgarsu tsakanin maboyar ‘yan ta’addan domin kauce wa farmakin jami’an tsaro.

Sojojin Amurka.
Dakarun rundunar sojojin Amurka aun fito aiki Hoto: U. S Navy
Source: Getty Images

Sojoji sun yi wa ISWAP babbar illa

Rahotannin sun kuma bayyana cewa an kashe wasu fitattun kwamandojin kungiyar yan ta'addan, ciki har da Abubakar Buduma, jagoran yankin Kirta Wulgo, wanda ya mutu bayan ya samu munanan raunuka.

Haka kuma, an kashe wasu masu sarrafa jiragen yaki marasa matuki da ake zargin suna da alaka da kungiyar ISIS, wadanda aka bayyana a matsayin Larabawa masu taimakawa ayyukan kungiyar.

An kuma lalata wasu cibiyoyin yada farfaganda da bayanan kungiyar yayin hare-haren, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

An kashe mayakan ISWAP 21 a Borno

A baya, kun ji cewa sojojin Amurka sun kara ba da gudummuwa wajen kai farmakin sama kan sansanin kungiyar 'yan ta'adda ISWAP a jihar Borno.

Harin sojojin na Amurka da na Najeriya ya kashe akalla mayakan kungiyar ISWAP 21 a yankin Arege da ke karamar hukumar Kukawa a jihar Borno.

Rahoton ya nuna cewa harin ya afkawa wani sansanin kungiyar ISWAP da ake zargin mayakan ke amfani da shi wajen shirya hare-hare a yankin Tafkin Chadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262