'Yan Ta'adda Fiye da 20 Sun Bakunci Lahira da Sojojin Amurka Suka Sake Kawo Dauki Najeriya
- Sojojin Amurka sun kara ba da gudummuwa wajen kai farmakin sama kan sansanin kungiyar 'yan ta'adda ISWAP a jihar Borno
- Rahoto ya nuna cewa harin ya yi sanadiyyar hallaka mayakan kungiyar ISWAP 21 a yankin Arege da ke karamar hukumar Kukawa
- Rahoton ya kara da cewa wannan farmakin wani bangare ne na ci gaba da hadin gwiwar da ke tsakanin Najeriya da Amurka wajen yaki da ta’addanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Borno, Nigeria - Rahotanni sun bayyana cewa sojojin Najeriya tare da hadin gwiwar rundunar sojin Amurka ta Afrika (US-AFRICOM) sun sake yin luguden wuta kan 'yan ta'adda a jihar Borno.
Harin sojojin na Amurka da na Najeriya ya kashe akalla mayakan kungiyar ISWAP 21 a yankin Arege da ke karamar hukumar Kukawa a jihar Borno.

Kara karanta wannan
"Kun tona wa kanku asiri," Wike ya taso Atiku, Peter Obi da Kwankwaso ana shirin zaben 2027

Source: Original
Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya, Zagazola Makama ya tabbatar da hakan a wani rahoto da ya wallafa a shafinsa na X.
Majiyoyi sun shaidawa Makama cewa an kai harin ne ranar Asabar bayan jami’an tsaro sun tattara bayanan sirri tare da gudanar da sa ido wanda ya tabbatar da taruwar mayakan kungiyar a yankin.
An kashe mayakan ISWAP 21
Rahoton ya nuna cewa harin ya afkawa wani sansanin kungiyar ISWAP da ake zargin mayakan ke amfani da shi wajen shirya hare-hare a yankin Tafkin Chadi.
A cewar majiyoyin tsaro, harin ya yi nasarar hallaka mayakan da dama tare da raunana karfin kungiyar wajen gudanar da ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.
"Harin da aka kai cikin kwarewa ya yi sanadin kashe ‘yan ta’adda 21 tare da janyo babbar illa ga ayyukan kungiyar," in ji majiyoyin.
Hadin gwiwar Najeriya da Amurka ta yi karfi
Rahoton ya kara da cewa wannan farmakin wani bangare ne na ci gaba da hadin gwiwar da ke tsakanin Najeriya da Amurka wajen yaki da ta’addanci da kuma rusa maboyar kungiyoyin masu tayar da kayar baya.
Majiyoyin sun bayyana cewa an tsara aikin ne bisa sahihan bayanan sirri, tare da aiwatar da shi cikin tsari domin kauce wa kura-kurai.

Source: Twitter
Rahoton The Cable ya ce wannan sabon farmaki na zuwa ne makonni kadan bayan wani jerin hare-haren sama da sojojin Najeriya da Amurka suka kai a yankin Metele na jihar Borno, wanda ya yi sanadin kashe fiye da mayakan ISIS/ISWAP 20.
Masana harkokin tsaro na ganin cewa ci gaba da irin wadannan hare-hare na iya kara raunana karfin kungiyoyin ta’addanci da ke addabar yankunan Arewa maso Gabashin Najeriya.
Amurka za ta yi bincike a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ware Dala miliyan 3.5 domin tallafa wa tattara bayanai da rahotannin tauye ‘yancin addini a Najeriya
Ta bayyana cewa shirin zai gudana na tsawon watanni 24 zuwa 48, kuma ana sa ran za a bayar da tallafin ga ƙungiya guda ɗaya ta hanyar tallafi ko haɗin gwiwar aiki.
Ma’aikatar Amurka ta ce manufar shirin ita ce ƙarfafa sa ido, tattara bayanai da rubuta rahotanni kan take hakkin addini da hukumomin gwamnati ko ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba ke aikatawa.
Asali: Legit.ng
