‘Yan ta’adda 150 sun mika wuya cikin mako guda a Arewa maso Gabas

‘Yan ta’adda 150 sun mika wuya cikin mako guda a Arewa maso Gabas

  • ‘Yan ta’adda sama da 150 sun mika wuya ga dakarun rundunar tsaro ta Operation HADIN KAI cikin mako guda da ya gabata
  • Rundunar ta ce yawan masu mika wuya ya ƙaru daga sama da 50 a makon da ya gabata a shiyyar Arewa maso Gabas
  • Rundunar ta danganta ci gaban da matsin lambar soji da ayyukan leƙen asiri da sauran matakan yaƙi da ta’addanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Rundunar Hadin Gwiwa ta Sojoji a Arewa maso Gabas, Operation HADIN KAI (OPHK), ta bayyana cewa ‘yan ta’adda 150 sun mika wuya cikin mako guda.

Rundunar sojin ta bayyana cewa wannan shi ne mafi girman adadin masu mika wuya da aka taɓa gani cikin mako guda a Arewacin Najeriya.

Sojoji.
Dakarun sojojin Najeriya da ke aikin wanzar da zaman lafiya Hoto: @NigerianArmy
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da rundunar sojojin ksa ta Najeriya ta wallafa shafin Facebook dauke da sa hannun Mukaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Rundunar Operation HADIN KAI, Kyaftin Mohammed Goni

Kara karanta wannan

Tinubu ya fusata da 'yan bindiga suka sace masallata a Neja, ya bayar da umarni

Yan ta'adda 150 sun mika wuya ga sojoji

Sanarwar ta ce adadin ya tashi daga kwamandoji, mayaka da masu alaƙa da ‘yan ta’adda 50 da suka mika wuya a makon da ya gabata zuwa sama da 150 a makon da ake ciki.

Kakakin rundunar ya ce ƙarin masu mika wuya na nuna tasirin ayyukan leƙen asiri da sojoji ke yi, ƙara matsin lamba kan ‘yan ta’adda da kuma haɗin gwiwar matakan soji da na farar hula da ake ɗauka domin rage ƙarfin ƙungiyoyin ‘yan ta’adda.

Sojoji sun matswa yan ta'adda

Goni ya ce wannan ci gaba na nuna cewa matsin lamba na ƙaruwa a cikin sansanonin ‘yan ta’adda, musamman kan ’yancinsu na zirga-zirga, samun kayan aiki, samar da abubuwan da suke buƙata da kuma iya riƙe mayakansu a maboyarsu.

Ya ƙara da cewa kwato makamai da alburusai daga wasu daga cikin waɗanda suka mika wuya na ƙara nuna tasirin matsin lambar da ake ci gaba da yi kan hanyoyin sadarwa da ayyukan ‘yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Bayan gargadin DSS, sojoji sun rika aman wuta a kan yan bindiga a Sokoto

A cewarsa, yawaitar masu mika wuya na nuna ƙara ingancin tsarin Operation HADIN KAI na yaƙi da ta’addanci, wanda ya haɗa ayyukan leƙen asiri, wayar da kai, hulɗa tsakanin sojoji da fararen hula da sauran matakan da ba na yaƙi ba.

Sojoji.
Dakarun sojojin Najeriya suna atisayen yaki a sansaninsu Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook
“Waɗannan matakai gaba ɗaya suna kawo cikas ga ayyukan ‘yan ta’adda da hanyoyin tallafa musu, suna raunana farfagandarsu tare da ƙarfafa ƙarin mutane su janye daga ta’addanci,” in ji shi.

Goni ya bayyana cewa ana tantance dukkan mutanen da suka mika wuya, a rubuta bayanansu tare da kula da su bisa ƙa’idojin da aka tanada da kuma dokokin da suka dace.

Sojoji sun ceto mutane 59 a mako 1

Kun ji cewa Hedikwatar Tsaron Najeriya (DHQ) ta sanar da nasarorin da rundunar sojoji ta samu cikin mako guda a sassa daban-daban naBNajeriya

A sanarwar da ta fitar, DHQ ta bayyana cewa sojoji sun ceto mutane 59 da aka yi garkuwa da su a cikin mako guda tare da kashe ’yan ta’adda 11.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262