Maganar Gwamnan Kwara Ta Tsokano Kungiyar Kwadago kan Mafi Karancin Albashi a Najeriya

Maganar Gwamnan Kwara Ta Tsokano Kungiyar Kwadago kan Mafi Karancin Albashi a Najeriya

  • Kungiyar NLC ta yi fatali da tayin N100,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi na ma'aikatan gwamnati a Najeriya
  • Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ne ya fara maganar karin albashin
  • Sai dai NLC ta ce ma'aikata sun cancanci a ba su albashin da bai gaza Naira miliyan 1 ba duba da matsin rayuwar da ake ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta yi fatali da yunkurin gwamnoni na kara mafi karancin albashin ma'aikata zuwa N100,000.

NLC ta bayyana cewa tayin mafi ƙarancin albashi na N100,000 da wasu gwamnoni suka yi bai dace da halin da ma’aikatan ƙasar ke ciki ba.

NLC da TUC.
Shugabannin manyan kungiyoyin kwadago na Najeriya, TUC da NLC suna jawabi a ranar ma'aikata Hoto: NLC HQ Nigeria
Source: Twitter

Kungiyar NLC ta bukaci albashin N1m

Kungiyar ta jaddada cewa ma’aikata sun cancanci samun har Naira miliyan 1 a wata idan aka yi la’akari da matsin tattalin arzikin da ake fama da shi a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Martanin Kwankwaso bayan samu tikitin takarar mataimakin Peter Obi a NDC

Mai magana da yawun NLC, Benson Upah, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai ranar Lahadi.

Tun da farko, Gwamna Abdulrahman AbdulRazaq na Kwara ya ce gwamnoni na duba yiwuwar amincewa da sabon mafi ƙarancin albashi na N100,000 domin rage wa ma’aikata radadin tsadar rayuwa.

NLC ta yi fatali da tayin N100,000

Sai dai NLC ta ce duk da cewa tunanin sake duba albashi abu ne mai kyau, adadin N100,000 ya yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da bukatun rayuwar ma’aikatan Nijeriya.

A cewar Upah, matsalolin tattalin arziki da suka haɗa da faɗuwar darajar Naira, hauhawar farashin kayayyaki, ƙarin kuɗin wutar lantarki, da tsadar fetur sun sanya ya zama dole a yi tunanin albashi mafi tsoka.

"Mun yaba da wannan tunani na gwamnan Jihar Kwara, amma gaskiyar magana ita ce N100,000 ba zai wadatar da ma’aikacin Nijeriya ba a wannan lokaci.
"Idan aka yi la’akari da matsalolin canjin kuɗi, hauhawar farashi, ƙarin kuɗin wutar lantarki, tsadar man fetur da sauran kuɗaɗen rayuwa, albashin da zai dace da ma’aikaci a yau zai kai kusan Naira miliyan 1 a wata," in ji shi.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun bukaci Tinubu ya dawo da mafi karancin albashi N100,000

Dalilin NLC na neman albashin N1m

Upah ya kuma yi nuni da cewa kuɗaɗen shiga da gwamnatoci ke samu a yanzu sun karu idan aka kwatanta da shekarun baya, don haka babu wani dalili da zai hana inganta walwalar ma’aikata.

Ya ce rabon kuɗaɗen da ake yi daga Asusun Tarayya (FAAC) ya ƙaru, yayin da wasu abubuwan da suka shafi kasuwar mai a duniya suka ƙara wa gwamnati kuɗaɗen shiga, kamar yadda The Cable ta kawo.

"A yau gwamnati na samun kuɗaɗen shiga masu yawa. Idan aka duba abin da ake rabawa jihohi daga FAAC, za a fahimci cewa akwai damar biyan ma’aikata albashi mai kyau.
Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Ma'aikata na goyon bayan NLC

Wani ma'aikacin gwamnatin tarayya, Saifullahi Ahmad ya shaida wa Legit Hausa cewa babu inda mafi karancin albashi na N70,000 yake kai wa a yanzu.

Ya ce duk da ya amimce da matsayar NLC na cewa N100,000 tayi kadan, amma batun neman akalla Naira miliyan 1 mafarki ne da a yanzu ba zai taba tabbatuwa ba.

Kara karanta wannan

ADC: 'Akalla 70% na yan Najeriya sun dawo daga rakiyar Shugaba Tinubu'

"Muna shan wahala musamman kananun ma'aikata, N150,000 zuwa N200,000 ba su daukar dawainiyar mu a yanzu, muna goyon bayan NLC ta shiga gaba domin a cimma matsayar da ta dace," in ji shi.

Yaushe za a fara tattaunawa kan albashi?

An ji cewa kungiyoyin ƙwadago a Najeriya sun bayyana cewa za su fara shirin sake tattaunawa kan mafi ƙarancin albashin daga watan Yulin 2026.

Shugabannin ƙungiyar NLC da TUC ne suka bayyana hakan a bikin ranar ma’aikata ta shekarar 2026 da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja.

Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce za a fara tattaunawa da wuri ne na da nufin tabbatar da cewa an kauce wa tsaiko da aka saba samu a tattaunawar albashi a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262