Abu Ya Girma: Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Dan Majalisar Tarayya daga Jihar Jigawa

Abu Ya Girma: Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Dan Majalisar Tarayya daga Jihar Jigawa

  • APC ta dakatar da 'dan Majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Auyo/Hadejia/Kafin Hausa, Hon. Usman Ibrahim tare da shugabanni
  • Hakan ya biyo bayan korafe-korafen da aka shigar kansu cewa suna gudanar da wasu ayyuka da suka saba wa kundin tsarin jam'iyya
  • APC ta umarci wadanda aka dakatar da su daina ayyana kansu a matsayin jami’ai ko wakilan jam’iyyar har sai an kammala bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jigawa, Nigeria - Jam’iyyar APC reshen jihar Jigawa ta dakatar da 'dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Auyo/Hadejia/Kafin Hausa, Hon. Usman Ibrahim, daga jam’iyyar.

Shugaban APC na jihar Jigawa, Ahmad Garba, ne ya sanar da matakin cikin wata sanarwa da aka fitar ga manema labarai ranar Litinin.

Jam'iyyar APC.
Tutar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Hoto: @OfficialAPC
Source: Twitter

A cewarsa, jam’iyyar ta dauki matakin ne bayan karbar korafe-korafe da rahotanni daga mambobinta kan zargin hannu a ayyukan da suka saba wa dokokin APC, kamar yadda Premium Times ta rahoto ba.

Kara karanta wannan

'Dan majalisar dokokin Kano ya bar tafiyar Kwankwaso, ya fice daga jam'iyyar NDC

Dalilin APC na dakatar da dan Majalisa

Sanarwar ta bayyana cewa ana zargin 'dan majalisar da wasu shugabannin APC a matakin mazaba da kananan hukumomi da aikata abubuwan da suka ci karo da manufofi da dokokin APC.

A cewar APC, ana zargin wadanda abin ya shafa da daukar matakan da za su iya bata sunan jam’iyyar, raunana ikon shugabancinta da kuma haddasa rikici tsakanin mambobi.

“Idan aka tabbatar da wadannan zarge-zarge, tonsun saba da sashe na 21.2 na kundin tsarin mulkin APC wanda ya haramta rashin biyayya ga wata jam’iyya da ayyukan da za su jefa ta cikin matsala,” in ji sanarwar.

APC ta dakatar da wasu jiga-jigai 6

Baya ga Hon. Usman Ibrahim, APC ta kuma dakatar da wasu shugabannin jam’iyyar guda shida.

Wadanda aka dakatar din sun hada da Aisha Adamu, mataimakiyar shugabar mata ta APC a jihar Jigawa, Yargabi Babannan, shugabar mata ta mazabar Auyo, da Musa Zabarau, shugaban APC na mazabar Auyo.

Sauran sune Ibrahim Ayama, mataimakin shugaban APC na karamar hukumar Auyo. Saje Hadiyau, sakataren kudi na APC a Auyo, Sani Hadiyau, mataimakin shugaban APC na mazabar Auyo.

Kara karanta wannan

Adamawa: Sarkin Mota ya samu takara a NDC, za a fafata da shi a zaben 2027

Jam'iyyar APC
Dan Majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Auyo/Hadejia/Kafin-Hausa ta Jigawa, Hon. Usman Ibrahim Hoto: Muh'd Aliyu Auyo
Source: Facebook

APC ta umarci wadanda aka dakatar da su da su daina ayyana kansu a matsayin jami’ai ko wakilan jam’iyyar har sai an kammala bincike.

Haka kuma an hana su halartar taruka ko gudanar da duk wani aiki da ya shafi APC a hukumance, tare da gargadin su da kada su yi wani abu da zai iya tasiri ga binciken da ake yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262