Wata Sabuwa: Matakin da Kasar Musulunci ta Iran Ta Dauka Zai Shafi Yan Najeriya

Wata Sabuwa: Matakin da Kasar Musulunci ta Iran Ta Dauka Zai Shafi Yan Najeriya

  • Amurka ta ce katsewar jigilar kayayyaki a mashigar Hormuz na iya taba kasashe irin Najeriya musamman kan batun abinci
  • Ana fargabar karancin takin zamani da tashin farashin makamashi zai kara tsadar noma da abinci a duniya sakamakon rufe Hormuz
  • Amurka ta ce karin farashin man fetur da takin zamani na iya jefa miliyoyin mutane cikin matsananciyar yunwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

United States - Amurka ta yi gargadin cewa matakin Iran na rufe mashigar Hormuz na iya kara tsananta matsalar karancin abinci a Najeriya da sauran kasashen yankin Afirka.

Wata jami’ar Amurka, Ambasada Jennifer Locetta, ce ta bayyana hakan yayin wani taron Majalisar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya kan matsalar karancin abinci da aka gudanar a New York.

Hormuz.
Mashigar ruwa ta Hormuz da ke karkashin ikon kasar Musulunci ta Iran Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

A rahoton Vanguard, Locetta ta ce hare-haren gwamnatin Iran a Mashigar Hormuz na kawo cikas ga kusan kashi daya bisa hudu na cinikin man fetur na duniya da kuma kusan kashi daya bisa uku na cinikin takin zamani a duniya.

Kara karanta wannan

Trump ya shiga matukar damuwa bayan rasuwar mawakiyar Amurka, Parton

Takin zamani na fuskantar cikas

Jami’ar ta ce takin zamani da aka hana wucewa ta mashigar Hormuz na da matukar muhimmanci ga samar da abinci a Afirka, kudu da Sahara, Kudancin Asiya da wasu sassan Kudu maso Gabashin Asiya.

Ta ce mashigar na daukar kusan kashi 20 cikin 100 na man fetur na duniya da kuma kusan kashi 33 cikin 100 na jigilar takin zamani a duniya.

Locetta ta ce hasashen raguwar noma a watannin da ke tafe na nufin karancin abinci, karin farashi da kuma karuwar yunwa a kasashe kamar Sudan, Najeriya da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.

Miliyoyin mutane za su shiga yunwa

Ta kuma ce karin farashin man fetur da aka samu sakamakon katsewar jigilar kayayyaki a mashigar ya fara yin illa ga ayyukan jin kai, kamar yadda tashar Al-Jazeera ta rahoto.

A cewarta, tashin farashin kayayyaki a yankunan da ake fama da rikici kamar Syria da Gaza na barazana ga nasarorin da aka samu wajen inganta samar da abinci ga al'ummomin da ke cikin mawuyacin hali.

Kara karanta wannan

An taso gwamnoni a gaba bayan FAAC ta cika aljihunsu da N47tr

Locetta ta ce Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, WFP, yanzu ta yi hasashen cewa karin mutane miliyan 45 za su shiga cikin matsananciyar yunwa a duniya sakamakon rikicin.

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wurin taron kasa da kasa Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Najeriya na dogara da takin waje

Gargadin Amurkan ya zo ne a daidai lokacin da ake kara nuna damuwa kan yadda rikicin Iran da Isra'ila ka iya tsananta matsalar karancin abinci a duniya zuwa shekarar 2027.

Bangaren noma na Najeriya na dogaro matuka da takin zamani da ake shigowa da shi daga kasashen waje, inda aka kiyasta cewa kusan kashi 70 na takin zamani da sauran muhimman kayan aikin noma ana samo su ne daga wajen kasar.

Mutanen Iran na cikin damuwa

A wani labarin, kun ji cewa shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce al’ummar kasar na fuskantar matsaloli da dama, musamman na tattalin arziki da rayuwa.

Pezeshkian ya ce gwamnatinsa na kokarin magance hauhawar farashi, rashin aikin yi da matsalolin rayuwa domin al’umma su samu damar rayuwa cikin mutunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262