"Rashin Zaben Tinubu na Iya Zama Zunubi," Gwamnan Delta Ya Ja Hankalin 'Yan Najeriya
- Gwamna Sheriff Oborevwori ya bayyana cewa al'ummar jihar Delta za su kada wa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kuri'unsu a zaben 2027
- Ya ce Shugaba Tinubu surukin Delta ne saboda alakar da ke tsakanin uwargidansa, Sanata Oluremi Tinubu da jihar
- Gwamnan ya kuma yabawa Oluremi Tinubu kan rawar da take takawa wajen karfafa dangantaka tsakanin gwamnatin tarayya da jihar Delta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Delta, Nigeria - Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya bayyana cewa mutannen jiharsa na tare da kudirin tazarcen shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a zabe mai zuwa.
Gwamnan ya yi ikirarin cewa zai iya zama zunubi babba idan al’ummar jihar Delta suka ki kada wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kuri’a a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Source: Facebook
Oborevwori ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da tashar talabijin ta Arise TV ranar Talata, inda ya jaddada cewa Shugaba Tinubu yana da alaka ta musamman da jihar Delta ta hannun uwargidansa, Sanata Oluremi Tinubu.
A cewarsa, daga cikin fitattun ‘yan takarar shugaban kasa da suka bayyana zuwa yanzu, Tinubu ne kadai ke da wata alaka kai tsaye da jihar Delta, lamarin da ya kamata ya sa ya samu cikakken goyon bayan mutanen jihar.
Wace alaka ta hada Bola Tinubu da Delta?
Da yake karin haske kan matsayinsa, gwamnan ya ce Shugaba Tinubu ba bako ba ne ga al’ummar Delta saboda kasancewar uwargidansa tana da asali daga yankin Warri da ke jihar.
“Daga cikin ‘yan takarar da suka bayyana, Bola Ahmed Tinubu ne kadai ke da alaka da jihar Delta. Mutumin surukinmu ne, kuma ba zai dace mu juya masa baya ba. Wannan lamari ne na iyali,” in ji Oborevwori.
Ya kara da cewa al’ummar yankin Neja Delta sun fara fahimtar muhimmancin wannan dangantaka, yana mai cewa yanzu mutane sun fi fahimtar inda muradunsu suke.
Gwamna ya yaba wa matar Shugaba Tinubu
Gwamnan ya kuma yabawa uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, kan rawar da take takawa wajen karfafa dangantaka tsakanin gwamnatin tarayya da al’ummar jihar Delta.

Source: Twitter
A cewarsa, uwargidan shugaban kasar ta samu karbuwa sosai musamman a tsakanin kabilar Itsekiri, inda ya yi ikirarin cewa hakan na kara wa shugaban kasa farin jini a yankin.
“Uwargidan shugaban kasa tana da matukar tasiri a Delta. Mutanen Itsekiri suna kallonta a matsayin ‘yar gida, kuma hakan yana kara dankon zumunci tsakanin Delta da gwamnatin tarayya,” in ji shi.
Tinubu zai samu kuri'un Arewa a 2027?
An ji cewa jigo a jam’iyyar APC a jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu gagarumar nasara a jihohin Arewa a 2027.
Kwankwaso ya danganta wannan hasashe da dimbin ayyukan raya kasa da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa a yankin Arewa, wadanda ya ce kudinsu ya kai tiriliyoyin Naira.
Daga cikin ayyukan da ya ambata akwai aikin titin Kano zuwa Kongolom mai tsawon kilomita 132, wanda aka ware masa sama da Naira biliyan 334.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

