Abin Mamaki da Bashir El Rufa'i ke Gani idan Ya Ziyarci Babansu da ke Tsare
- Ɗan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce duk lokacin da ya ziyarci mahaifinsa a tsare yana mamakin irin ƙarfin zuciya da jajircewar da yake nunawa
- Ya ce El-Rufai ya tabbatar masa cewa har yanzu yana ganin sadaukarwar da ya yi ta dace, inda ya amsa da cewa “eh” ba tare da wani jinkiri ba
- Kalamansa sun jawo martani daga masu amfani da kafafen sada zumunta, yayin da wasu ke addu'ar samun 'yancin El-Rufai a nan gaba kadan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya bayyana yadda yake ji bayan kai wa mahaifinsa ziyara sau da dama a wurin da ake tsare da shi.
Ya ce abin da ke ba shi mamaki shi ne yadda waɗanda ke wajen wurin tsarewar suka fi nuna damuwa, alhalin El-Rufai da kansa yake ci gaba da nuna ƙarfin hali da walwala duk da halin da yake ciki.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanan da Bashir El-Rufa'i ya yi ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a rana Laraba, 26 ga Agustan 2026.
Ɗan El-Rufai ya yi magana
A wani sako da ya wallafa, ɗan tsohon gwamnan ya ce duk lokacin da ya ziyarci mahaifinsa, yakan bar wurin cikin mamakin yadda El-Rufai ke da ƙarfin gwiwa da kuma yanayi na farin ciki.
Ya ce har yanzu mahaifinsa yana yin barkwanci kamar yadda ya saba, lamarin da ya sa shi yin tunani kan yadda yake iya jurewa duk da kasancewarsa a tsare.
Ya ce ya tambayi mahaifinsa ko har yanzu yana ganin sadaukarwar da ya yi ta cancanci abin da yake fuskanta. A cewarsa, El-Rufai bai yi wata-wata ba wajen ba da amsa, inda ya ce:
“E.”
Martani ya biyo bayan kalaman
Kalaman nasa sun haifar da martani daga mutane da dama a kafafen sada zumunta, inda wasu suka yaba da jajircewar tsohon gwamnan tare da addu'ar samun 'yancinsa.

Kara karanta wannan
Zance ya ƙare, Peter Obi ya bayyana matsayarsa kan batun dawo da tallafin man fetur a Najeriya
Nuhu Aminu ya ce:
“In sha Allah sadaukarwar ta cancanta kuma za a sake shi. Zai sake rubuta tarihi a matsayin wanda ya taka rawa wajen gina sabuwar Najeriya.”
Shi ma Bashir Garba Sufyan ya bayyana El-Rufai a matsayin mutum mai tsayawa kan ƙa'idojinsa duk da irin halin da yake ciki.
Ya ce:
“A koyaushe nakan tambayi kaina ko mutanen da ya yi wa wannan sadaukarwar sun cancanci hakan. Amma Alhamdulillah, Malam mutum ne mai tsayin daka kan abin da ya yi imani da shi.”
Austin Idoko ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda siyasa za ta iya raba mutane, yayin da Mai Kudi Usman ya buƙaci El-Rufai ya ci gaba da jajircewa.

Source: Facebook
An nemi yi wa El-Rufa'i adalci
A wani labarin, mun ruwaito cewa jagoran ADC, Jafar Ibrahim Sani, ya bukaci dattawan Arewa da shugabannin siyasa su tabbatar da adalci da bin ka'idojin doka a batun da ya shafi Nasir El-Rufai.

Kara karanta wannan
Atiku ya ɗauki zafi, ya sake fallasa abin da yan Najeriya ba su sani ba kan tallafin man fetur
Legit Hausa ta rahoto cewa Jafar Sani ya ce bai kamata bambancin ra'ayin siyasa ya zama dalilin watsi da adalci ko kin tabbatar da hakkin kowa ba.
Ya kuma bayyana cewa ya kamata halin da El-Rufai yake ciki ya zama darasi kan irin siyasar da ake son gina wa al'ummomin Najeriya a nan gaba.
Asali: Legit.ng
