'Ba Ku da Maraba da Almajirai': Jigon ADC ga Masu Daukar Albashin N300,000

'Ba Ku da Maraba da Almajirai': Jigon ADC ga Masu Daukar Albashin N300,000

  • Jigon ADC a Najeriya ya shawarci ma’aikata a birnin tarayya Abuja su nemi karin hanyoyin samun kudin shiga
  • Ɗan APC ya ce faduwar darajar naira ta rage karfin saye, yayin da tsadar abinci, haya da sufuri ke wahalar da ma’aikata
  • Ya ce albashin kasa da N300,000 a Abuja na iya hana mutum samun rayuwa mai kyau, saboda hauhawar kudin bukatun yau da kullum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wani jigon jam'iyyar ADC, Usman Austin Okai, ya shawarci mazauna Abuja masu daukar albashi.

Ɗan ADC ya ce masu samun kasa da N300,000 duk wata su nemi karin hanyoyin samun kudin shiga.

Jigon ADC ya koka kan matsin tattalin arziki
Jigon ADC, Usman Austin Okai da ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar, Atiku Abubakar. Hoto: Usman Austin Okai.
Source: UGC

Okai ya bayyana hakan ne a wani sakon Facebook, inda ya ce faduwar darajar naira ta rage karfin sayen ma’aikata, tare da kara wahalar biyan bukatunsu.

Kara karanta wannan

An taso gwamnoni a gaba bayan FAAC ta cika aljihunsu da N47tr

Matsalolin da ma'aikata ke fuskanta a Abuja

A cewarsa, ma’aikatan Abuja da ke samun kasa da N300,000 na iya fuskantar matsalar samun rayuwa mai inganci saboda tsadar haya, abinci da sufuri.

Okai ya rubuta cewa:

"Idan albashinka bai kai akalla N300,000 a Abuja ba, bambancinka da Almajiri faranti ne kawai. Kasuwanci ya fi zama mafita yanzu. An lalata kudinmu.”

Gidaje na daga cikin manyan abubuwan da ke cinye kudin mazauna Abuja, musamman a yankunan da ake matukar neman gidaje kamar Wuse, Maitama da Asokoro.

Jigon ADC ya ba ma'aikata shawara
Jigon jam'iyyar ADC a Najeriya, Usman Austin Okai. Hoto: Usman Austin Okai.
Source: Facebook

Matsin tattalin arzikin Najeriya ya shafi ƴan Abuja

Mazauna yankunan Lugbe, Kubwa da Nyanya ma na fuskantar tsadar kudin haya na shekara, lamarin da ke kara matsin tattalin arziki.

Farashin abinci ma ya kara matsin lamba kan kasafin iyalai, yayin da kayan masarufi kamar shinkafa, kwai, burodi da tumatir suka kara tsada.

Haka kuma, farashin man girki, kaji da sauran kayan abinci ya karu, abin da ke sa iyalai kashe karin kudi wajen samun abinci.

Kara karanta wannan

Zance ya ƙare, Peter Obi ya bayyana matsayarsa kan batun dawo da tallafin man fetur a Najeriya

Kudin sufuri ma ya tashi, lamarin da ya shafi ma’aikatan da ke yin zirga-zirga kullum daga gidajensu zuwa wuraren aikinsu.

Yadda cire tallafi ya shafi tattalin arziki

Karin farashin fetur bayan cire tallafin man fetur a shekarar 2023 ya taimaka wajen kara kudin sufuri da farashin zirga-zirgar jama’a.

Hada tsadar abinci da sufuri, faduwar darajar naira da karin kudin haya ya ci gaba da matsa wa kudaden shiga iyalai lamba.

Wannan matsin ya fi shafar masu karamin da matsakaicin karfin samun kudin shiga da ke zaune a Abuja, saboda tsadar rayuwa a babban birnin.

Tsare El-Rufai: Jigon ADC ya shawarci dattawan Arewa

An ji cewa Jafaru Ibrahim Sani ya bukaci dattawan Arewa da shugabannin siyasa su duba batun Nasir El-Rufai ba tare da bambancin siyasa ba.

Tsohon mataimakin shugaban ADC na shiyyar Arewa maso Yamma ya ce adalci da bin ka’ida su zama ginshikin yadda ake tunkarar lamarin tsohon gwamnan Kaduna.

Jafaru Sani ya ce halin da El-Rufai ke ciki ya kamata ya sa Arewa ta yi tunani kan irin siyasar da take ginawa ga al'umma masu zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.